Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce, ‘yan daba sun tarwatsa aikin zabe a Jihar Delta da Katsina, inda suka yi awon gaba da na’urar tantance masu zabe BVAS har guda takwas.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai a ranar Asabar.
- Zaben 2023: Atiku Ya Lashe Mazabar Shugaban Majalisar Dattawa A Yobe
- Zaben 2023: Peter Obi Ya Lashe Akwatin Mazabarsa A Anambra
Ya yi bayanin cewa, a karamar hukumar Oshimili da ke jihar Delta, ‘yan daban sun kai hari rumfar zabe tare sannan suja sace na’urar BVAS guda biyu.
Kazalika, ya kara da cewa, a karamar hukumar Safana da ke Jihar Katsina, ‘yan daban sun hari kan wata cibiyar kada kuri’a tare da yin awon gaba da na’urar BVAS guda shida, amma a cewarsa jami’an tsaro sun samu nasarar kwato guda uku daga cikin shidan da aka sace.
Sannan, ya nuna takaicinsa cewa yanzu ‘yan daban siyasa sun koma harar mashin din BVAS.
Mahmood ya cigaba da cewa aikin da ke rataye a kan hukumar shi ne tabbatar an gudanar da zaben ingatacce kuma sahihi wanda zai karbu.
A cewarsa, “A karamar hukumar Oshimili da ke jihar Delta, ‘yan daba sun farmaki rumfar zabe suka sace mashinan BVAS biyu a lokacin da aikin zaben ke gudana. Amma a bisa kokarinmu, nan da nan muka samu nasarar maye gurbin na’urorin da aka sace, tare da kara jibge jami’an tsaro kuma zabe ya cigaba da gudana.
“Sannan, a karamar hukumar Safana a jihar Katsina nan ma ‘yan daba sun farmaki rumfar zabenmu tare da sace BVAS 6. Amma mun samu nasarar kwato wasu, sannan an kara zuba jami’an tsaro kuma zaben ya cigaba da gudana kamar yadda aka tsara a wannan wurin.”
Ya ce, wannan shine karo na farko tun babban zaben 2011 da aka sanya zabe aka gudanar ba tare da dagewa ba.
“Mun tabbatar mun dage wajen cigaba da gudanar da abubuwan da suka dace. Zuwa yanzu mun samu nasarori sosai a yayin zaben nan kuma hanyar amfani da na’urar BVAS an samu aiki mai inganci.”