Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce zaben 2027 zai kasance ne tsakanin mulkin Shugaba Bola Tinubu da kuma zabin mutanen Nijeriya.
Ya zargi Shugaba Tinubu da gwamnatinsa da yin mulkin kama-karya ba tare da la’akarin cewa talakawa ne suka zabi gwamnatin ba. Sannan kuma ya zargi gwamnatinn Tinubu da haifar da wani matsala na hana ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda a cewarsa, hakan na gaba da raunana tsarin mulkin dimokuradiyya a kasar nan.
Atiku ya ce rashin samun ci gaba ya kamata ya damu kowane dan Nijeriya, yana cewa idan har aka ci gaba ba a haka, a karshe zai gwamnatin tarayya ta zama mai zalunta sakamakon dake hakkin ‘yan kasa da mayar da su bayin gwamnati.
“A tsawon watanni da dama, kungiyoyin kare hakkin Dan’adam na cikin gida da na kasa da kasa sun jawo hankali kan tsarin mulkin Tinubu na kama-karya.
“A karkashin tsarin doka, wannan gwamnati tana amfani da wani babban iko mai tsanani wanda yake samar da tsoro kuma yake neman shafe ‘yancin fadin albarkar baki da ke tallafa wa dimokuradiyya. Wannan wani abin mamaki ne, cin mutuncin ‘yanci ne, kuma dole ne a ki shi gaba daya.
“Ana kiransa da suna dokar binciken tntanet ta tsoratarwa, wadda kasashen da suka ci gaba da dama suka dade da yin watsi da ita. A karni na 21, ba za a iya tunanin cewa gwamnatin Nijeriya za ta tauye ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda shi ne ginshikin mulkin dimokuradiyya.”
Atiku ya ce duk wata doka da ke take ‘yancin ‘yan kasa na yin tsokaci mai muhimmanci game da shugabanninsu ko a hanyoyin sadarwar zamani ko ta hanyar magana ba dimokuradiyya ba ce kuma kai tsaye take hakkokin Dan’adam ne.
“A cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata tun bayan da gwamnatin Tinubu ta fara daukan matakan da ke janyo kuncin tattalin arziki da yunwa da bakin ciki ga mutanen Nijeriya, mun shaida zanga-zanga da koke-koke daga ‘yan kasa da ba za su iya daukar mulkin rashin gaskiya ba. Duk da haka, maimakon sauraron ‘yan kasa sai gwamnatin ta zabi hanyar amfani da karfin hukumo da tsoratarwa wadda ta juya lamarin zuwa wani abu daban.
“Lallai abin bakin ciki ne na ganin ana take hakkin ‘yan kasa da kundin tsarin mulki ya tabbatar a lokacin da ya kamata dimokuradiyyarmu ta kasance mai bin tsari. Dole ne mu tunatar da gwamnatin Tinubu cewa babu gwamnati a lokacin da ta kasa kare ‘yancin ‘yan kasarta, komai karfinta kuwa. Yin haka abun ta da hankali ne kuma hakan yana nuna gazawar gwamnati a fili.”
Atiku ya ce tabbas gwamnati na da alhakin kula da doka da oda, babu ingantacciyar gwamnati da za ta harbi masu zanga-zangar lumana da harsashi mai rai ko ta boye a bayan dokoki tana musguna wa ‘yan kasa.
Ya ce rashin kulawar gwamnati Tinubu ga dokar kasa da kuma ci gaba da kin bin umarnin kotu sun zama shahararrun siffofinta mafiya suna a kasar nan a halin yanzu.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kara da cewa tun farkon wannan gwamnati, kungiyar kare hakkin Dan’ada ta Amnesty ta soke wannan gwamnatin da take hakkin Dan’adam.
Ya ce haka ma wasu kungiyoyi masu muhimmanci kamar irinsu kungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya da kungiyar kare ajandar kafafen yada labarai sun yi korafi kan cin zarafin ‘yan jarida da ‘yan kasa ta hannun jami’an gwamnati.
 
			




 
							








