Wasu rahotanni na tabbatar da rasuwar daya daga cikin deliget na jihar Jigawa kuma shugaban jam’iyyar APC na shiyyar jigawa ta tsakiya Alh Isah Baba buji.
Babuji ya rasu gabanin fara zaɓen fitar da gwani na dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a birnin tarayya, Abuja.
A Labarin rasuwar ya da muka samu an tabbatar da cewa, ya rasu ne bayan wata gajeriyar rashin lafiya da ta iske shi a Abuja yayin da ake dab da fara gudanar da zaɓen fitar da ɗan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC.
Talla
Muna Addu’ar Allah ya gafarta masa.
Talla