Darakta-janar na kwamitin yakin neman zaben Yemi Osibanjo, Sanata Kabiru Gaya, ya ce, wasu ‘yan takarar tikitin kujerar Shugaban kasa na jam’iyyar APC su uku sun cimma matsayar janye wa, Yemi Osinbajo.
Ya ce, yanzu haka adadin masu fafatawar ya ragu zuwa mutum biyu Osinbajo da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Gaya, shi ne Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta kudu, ya shaida wa gidan talebijin na Channels cewa, yanzu adadin masu takara mutum biyu ne kawai, sai dai bai bayyana sunayen mutum biyu daga cikin wadanda suka janye din ba, sai dai ya ce tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ken Nnamadi ya janye wa Osinbajo din.
Gaya ya ce: “Muna da mataimakin shugaban kasa, Osinbajo da Bola Tinubu masu takara. Ina da cikakken masaniyar cewa wasu daga cikin ‘yan takarar sun janye wa Osinbajo da suka hada da Nnamani da wasu biyu da suka janye wa Osinbajo.”
Idan za ku iya tunawa dai, gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong da safiyar ranar Talata ya tabbatar da cewa, jerin sunayen ‘yan takara biyar ne suka aike wa shugaba Muhammadu Buhari domin fitar da mutum guda a cikin su.
Mutum biyar din su ne Tinubu, Osinbajo, Gwamna Kayode Fayemi na Ekiti da takwaransa na Ebonyi, Dave Umahi; da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.