Gamayyar ‘yan takara da suka fito daga sauran manyan jam’iyyu a Jihar Kaduna, sun goyi bayan takarar Rt. Honorabil Yusuf Dahiru Liman a zaben cike gurbi da za a yi a ranar 3 na watan Fabrairu, 2024.
Za a yi zaben ne a mazabu biyar a Makera, wanda Liman ya fito, da ke a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a zaben majalisar dokokin jihar.
- Bach Ya Yi Imanin Cewa CMG Zai Yi Ingantaccen Aiki Game Da Wasannin Olympics Na Paris
- Firimiyar Ingila:Yadda Liverpool Ta Fama Raunin Chelsea A Anfield
Daya daga cikin ‘yan takarar kuma wanda ya yi magana a madadin sauran ‘yan takarar, Honorabil Nura Mohammed Sarki ne, ya bayyana hakan a taron menema labarai da ‘yan takarar suka kira a Jihar Kaduna.
Sun sanar da cewa Liman na da kyawawan halaye da kwarewa da sanin iya gudanar shugabanci wajen ciyar da mazabar Makera gaba da kuma daukacin fadin Kaduna.
Kazalika, ‘yan takarar sun bukaci da a gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaben cike gurbin tare da kuma yin kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da an gudanar da zaben a cikin kwanciyar hankali da lumana.