Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta ci gaba da zama ta daya a teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila bayan da suka doke Chelsea da ci 4-1 a filin wasa na Anfield.
Chelsea wadda ta fara wasan da zimmar samun maki domin ci gaba da farfadowa a gasar ta Firimiya, ta kare wasan a matsayi na 10 akan teburin gasar.
- Hukuncin Zaben Adamawa: Na Rungumi Kaddara – Binani
- ‘Yansanda Sun Kama Dan Bindiga, Sun Ki Karbar Cin Hancin Miliyan 8 A Taraba
Diogo Jota, Conor Bradley, Sodbozslai da Luis Diaz ne suka jefawa Liverpool kwallaye 4 a ragar Chelsea, inda sabon dan wasan Chelsea Christopher Nkunku ya farke mata kwallo daya tilo a wasan.
Hakan yasa Liverpool wadda take bankwana da koci Jurgen Klopp ta dare akan teburin gasar Firimiya da maki 51, maki biyar tsakaninsu da Manchester City dake matsayi na biyu.