Jam’iyyar PDP ta ce za ta kai kara kotu game da sakamakon zaben gwamnan Jihar Edo da aka yi a karshen mako.
A ranar Lahadi ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana dan takarar APC, Monday Okpebholo, a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u 291,667.
- CMG Ya Gabatar Da Bikin Baje Shirin Bidiyo A Moscow Albarkacin Bikin Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Janhuriyar Jama’ar Sin
- Xi Ya Bukaci A Ci Gaba Da Inganta Hadin Kai Tsakanin Kabilu A Dukkan Zuri’o’i
Sai kuma dan takarar PDP mai mulkin jihar, Asuerinme Ighodalo, wanda ya zo na biyu da kuri’u 247, 274.
Da yake magana yayin wani taron manema labarai a Abuja, mukaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagun ya nemi hukumar zabe ta sake duba sakamakon.
“Duk da tashin hankali, da tilastawa, da magudin da APC ta yi, sakamakon da muka tattara daga rumfunan zabe sun nuna karara dan takararmu Ighodalo ne ya ci zaben da kafin a sauya sakamakon a cibiyar tattarawa ta jiha,” a cewarsa.
A cewarsa, matakin da kotuna suka yanke game da korafin da za su shigar ne “zai tantance ko har yanzu ‘yan Nijeriya na alfahari da kasarsu ko kuma a’a”.