Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta lashi takobin maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kan zaben da aka gudanar na shugaban kasa da na gwamna.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar a jihar, Ahmad Aruwa ya fitar a ranar Alhamis.
- Gobara Ta Tashi A Kasuwar Sayar Da Kayan Motoci A Legas
- Kugiza Kaheru: Shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” Na Haifar Da Ci Gaba A Nahiyar Afrika
Aruwan ya ce jam’iyyar bayan gudanar da taro, ta yanke hukuncin shiga kotu don neman hakkinta a can.
Tun da fark jam’iyyar ta bukaci INEC da ta sake duba sakamakon zaben gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, inda ta ce zaben ya fi dacewa a ayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba, kamar yadda aka yi a jihar Adamawa da Kebbi.
APC ta ce adadin kuri’un da Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya bai wa dan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna ba su kai adadin wadanda aka soke ba.
Bayan INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben, jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar sun shiga zanga-zanga inda suka bukaci a ayyana zaben a matsayin ‘Inconclusive’.
A ranar Laraba ne dai INEC ta bai wa Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo takardar shaidar lashe zaben gwamna da mataimaki da aka gudanar a jihar.