‘Yan bangar siyasa sun lalata katinan dangwala kuri’a a wasu rumfunar zabe a Jihar Zamfara.
Sannan, sun kuma kai wa Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka na Jihar Zamfara, Hon Rabi’u Garba Gusau a lokacin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a Gusau babban birnin jihar a ranar Asabar.
- Matashin HK Ya Bayyana Kwarin Gwiwa Kan Kwanciyar Hankalin Yankin A Taron MDD
- An Kashe Mutane Shida Kan Zargin Sace Akwati A Benuwe
‘Yan bangar sun kai farmaki ne a mazabar Birnin Ruwa dauke da makamai a rumfar da shi Kwamishinan ya ke kada kuri’arsa.
Haka zalika, ‘yan bangar siyasa sun fatattaki masu kada kuri’a daga kan layi tare da kwace kuri’un zabe, lamarin da ake tunanin sun yi hakan don sun fahimci wanda suke so ba shi ne ke samun kuri’u a wannan mazabar ba.
An bayyana cewa kwamishinan ya samu cece-kuce da wasu ‘yan bangar siyasa na jam’iyyar adawa a rumfar zabensa inda daya daga cikinsu ya bugi kansa ya raunata shi.
Wanda abin ya faru a gabansa ya shaida wa manema labarai cewa sai da jami’an tsaro suka shiga tsakaninsu don ceto Kwamishinan daga farmakin ‘yan bangar siyasar.
Bayan ceto sa da jami’an tsaron suka yi an garzaya da shi zuwa wani asibiti domin yi masa magani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp