Dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, Manjo Janar Aminu Bande, ya yi alkawarin kafa cibiyar sana’o’i don karfafawa matasa da kuma shawo kan matsalar rashin aikin yi idan aka zabe shi.
Ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da manema labarai a ofishin yakin neman zabensa da ke Birnin Kebbi.
- ‘Yan Takarar Gwamna Daga Jam’iyyun Adawa 7 Sun Janyewa Ashiru Na PDP A Jihar Kaduna
- Timi Frank Ya Bukaci Shugaban INEC, Yakubu, Ya Yi Murabus
Bande ya ce za su samar tsangayar koyar da sana’o don koyar da sana’o’in da suka dace ga wadanda suka kammala karatun digiri da wadanda ba su kammala karatu ba daga bangarori daban-daban na rayuwa.
Ya ce: “Halin da ake ciki yanzu a duniya, shi ne koyon sana’o’i, dole ne mu nemo hanyar da za mu ilimantar da ‘ya’yanmu domin su samu sana’o’in da za su iya kula da kansu ba tare da dogaro da gwamnati wajen neman aiki ba.
“Za su koyi komai a cibiyar da za a kafa daga dafa abinci; kafinta, injiniyanci, gine-gine da gyaran mota da sauransu. Abu ne da kowa zai yi alfahari da shi”.
Janar Bande ya ce cibiyar sana’o’in idan aka kafa ba kawai za ta samar da guraben ayyukan yi ba ne, za ta hada kan matasa gaba daya tare da sauya su zuwa matsayin masu aikin da za su iya daukar ma’aikata.