Babbar Kotun Tarayya da ke da zamanta a garin Osogbo a jihar Osun ta dakatar da jami’an tsaron Amotekun daga gudanar da ayyukan samar da tsaro a yayin zaben gwamnan da za a gudanar a gobe Asabar.
- Har ila yau, kotun ta umarci INEC kar ta yi amfani da kungiyar ta Amotekun a lokacin zaben na gobe.
- Zaben Osun: Yadda Mawaki Portable Ya Sha Suka Kan Goyon Bayan APC
- Ziyarar Kabarin Annabi (SAW) 1
Umarnin na kotun ya kuma gargadi Amotekun kar ta yi wani aikin sa kai a lokacin gudanar da zaben.
Da yake yin martani kan hukuncin na kotun, Hashim Abioye, ya sanar da cewa, biyo bayan wannan umarnin na kotun, hukumar zaben ba ta da wani hurumin yin amfani da jami’an tsaron Amotekun a matsayin mai wanzar da tsaro a yayin zaben na kujerar gwamna a jihar
Abioye ya ce, “A maganar nan da nake yi a yanzu, wadanda INEC za ta yi amfani da su sune, ‘yan sanda da kuma sauran hukumomin tsaro kawai a jihar”.