ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben Shugaban Kasa: A Shirye Mu Ke Mu Bayar Da Duk Bayanan Da Kotu Ta Bukata – INEC

by Sulaiman
3 years ago
INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa a shirye ta ke ta damƙa kwafen bayanai da dukkan kayan da kotu ta bayar da umarni ga jam’iyyu ko ‘yan takarar da ke ƙorafi kan zaɓen ranar 25 ga Fabrairu, domin su yi nazarin da su ke so su yi.

Shugaban hukumar ne, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, lokacin da ya karɓi tawagar lauyoyin jam’iyyar LP bisa jagorancin Babban Lauya Livy Uzoukwu.

ADVERTISEMENT
  • Ba Za Mu Amince Da Gazawar Kwamishinonin Zabe Bayan Daidaita Na’urar BVAS Ba – Shugaban INEC

Tawagar ta lauyoyin na LP dai sun ziyarci Hedikwatar INEC ce a ranar Litinin, a Abuja.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Yakubu ya tabbatar masu da cewa ya karɓi wasiƙar da LP ta aika masa a ranar 6 ga Maris, wadda ta sanar da shi cewa lauyoyin ta za su kai ziyara INEC domin duba kayan zaɓe.

Ya ce wasiƙar na ɗauke da ƙarin bayanin sanar da shi cewa ya sanar da Kwamishinonin Zaɓe na INEC da ke a kowace jiha, cikin jihohi 36 na faɗin ƙasar nan da FCT Abuja.

Wasiƙar dai ta nemi INEC ta umarci Kwamishinonin Zaɓe na jihohin su damƙa wa LP bayanai da kayan da ta ke buƙata domin gabatar da bayanan ƙarar ta a kotu.

Yakubu ya ce INEC ta shirya gudanar da taro da Kwamishinonin Zaɓe, domin su tattauna batutuwa da dama, ciki har da batun bayar da sahihan kwafe-kwafe na bayanan zaɓe ga dukkan waɗanda su ka shigar da ƙara, ba ma ga LP ita kaɗai ba.

“Ina tabbatar maku da cewa INEC ba ta wani nuƙu-nuƙun ɓoye komai. Za mu ba ku dukkan abin da ku ke buƙata.

“Kwafen bayanai biyu ne ke a hannun Hedikwatar INEC nan a Abuja. Kuma za mu iya samar maku waɗannan kwafen ba tare da ɓata lokaci ba. Akwai kwafen sakamako na EC8Ds da aka tattara daga jihohi da kuma mai lamba EC8DA, wanda sakamakon zaɓe ne da INEC da kan ta ta tattaro daga cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.

“Mai lamba EC8DA dai ina jin kwafe 39 ne. Kuma za mu iya samar maku kwafen su ba tare da ɓata lokaci ba,” inji Yakubu.

Ya ce sauran kwafen bayanai kuma duk su na ofisoshin INEC na jihohi daban-daban, kuma hukumar za ta so sanin ranakun da lauyoyin za su je jihohi domin a shirya masu kwafen kafin su isa, yadda su na zuwa sai dai su fara nazari kawai’.

“Sauran bayanai kuma alƙaluma ne lambobi da bayanan tantance mai shaidar katin rajistar zaɓe na rumfunan zaɓe fiye da 176,000.

“Za mu samu lokaci mu buga kwafe-kwafen su a wadace, sannan mu damƙa maku cikin hanzari.”

Daga nan ya shawarci tawagar lauyoyin INEC su gana da lauyoyin INEC domin su bayyana wa juna batutuwa da dama.

Jagoran tawagar lauyoyin LP, Uzoukwu ya shaida wa Yakubu cewa dalilin ziyarar shi ne domin su share hanyar fara nazarin kayan zaɓen shugaban ƙasa. “Saboda ka san dai mu na da kwanaki 21, waɗanda a cikin su ne za mu shigar da ƙara, a madadin waɗanda mu ke karewa. Yanzu kuma daga cikin kwanaki 21 ɗin, kusan kwanaki 10 kaɗai ne su ka rage mana. Ga shi kuma har yau ɗin nan ba mu karɓi kwafen takardun bayanai ko kayan zaɓe ko da guda ɗaya ba.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
Binciken Kayan Zabe: Atiku Ya Janye Sabbin Ƙorafe-Ƙorafe Da Ya Shigar A Kan INEC

Binciken Kayan Zabe: Atiku Ya Janye Sabbin Ƙorafe-Ƙorafe Da Ya Shigar A Kan INEC

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.