Gamayyar kungiyoyin farar hula a Nijeriya, a ranar Talata, sun gudanar da zanga-zanga zuwa hedikwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), inda suka bukaci shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu da ya yi murabus daga mukaminsa cikin gaggawa.
Gamayyar kungiyar kungiyoyi masu zaman kansu wacce ta kunshi kungiyoyi 18, ta kuma bukaci a binciki dalilan da suka sa INEC a karkashin Farfesa Yakubu ta kasa cimma ‘yancin dimokuradiyya musamman a lokacin zaben shugaban kasa da aka kammala.
Da yake jawabi ga manema labarai yayin zanga-zangar da aka gudanar a hedikwatar hukumar ta INEC a gundumar Maitama da ke Abuja, babban jagoran zanga-zangar, Dada Olayinka, ya ce ‘yan Nijeriya ba za su amince da duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaben kasar nan ba.
Kungiyoyin sun hada da Civil Society Forum of Nigeria, Nigeria Youth Development Forum, Democratic Youth Initiative, Forum for Social Justice, Movement for the Development of Democracy and Safeguard Nigeria Movement.
Sauran sun hada da Alliance for People’s Welfare, Forward Nigeria Movement, Human Right Crusaders, Defenders of Democracy, Democratic Rights Assembly da kuma Voter’s Rights Assembly.