Zainab A – Obaid Youssef ta kasance mace Injiniyar Jiragen Sama a kasar Sudan daga (1952 zuwa 19 ga Maris, 2016), kuma ita ce mace ta farko da ta samu lasisin haka daga hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar Birtaniya.
Ta yi aiki a Kamfanin Jiragen Sama na Sudan daga Yulin 1973 zuwa Mayun 1992 wanda bayan nan ta koma Birtaniya da zama. A shekarun 1960, matan Sudan da ke kokarin karatu da aiki a wasu bangarori ciki har da sashen injiniya sun gamu da tasku saboda yanayin al’adun mutanen kasar. Sai dai duk da haka, Zainab ta jajirce har ta yi karatu da kuma aiki a bangaren da ya shafi lantarki da aikin injiniyar jiragen sama. Daga nau’o’in jiragen da Zainab ta yi aiki a kansu akwai samfurin Boeing 707, Boeing 737/347/Boker 50 da Boker F27 duk a Kamfanin Jiragen Sama na Sudan, sai kuma samfurin Cessna 402/404/208 da kuma Bitchcraft 1900 na Kamfanin Kudancin Landan.
- Kungiya Ta Shirya Taro Kan Na Bunkasa Kimiyyar Karatu Daga Nesa
- Dala Biliyan 95! Shin Da Gaske Kasar Amurka Tana Da Karamci?
An haifi Zainab a Birnin Khartoum a ranar 23 ga watan Yuni a shekara ta 1952. Ita ce ‘ya ta farko ga mahaifinta Al-Abeed Yaussef Ahmed Shadewan, sanannen dan kasuwa da ake matukar girmamawa a Birnin, iyayenta, uwa da uba duk sun kasance masu riko da addini.
Ta taso ce a kauyen Um Dawa Ban da ya yi fice da Makarantar Al Masid, katafariyar makarantar koyar da Alkur’ani mai girma ga yara maza inda mutane a daukacin Sudan da yankin sahara na kudancin Afirka ke tururuwar kai ‘ya`yansu domin koyon karatun Alkur’ani. Zainab ta kammala karatunta na matakin Sakandare bisa kwarin gwiwar da ta samu daga mahaifinta, saboda a wancan lokacin bisa al’adar Sudan, yarinya mai irin shekarunta kan dakatar da karatun da take yi ta yi aure.
Zainab dai ba ta tsaya ba har sai da ta cimma burinta na karanta fannin aikin Injiniyan lantarki a Jami’ar Khartoum daga shekarar 1970 zuwa 1973.
Ta yi aiki a matsayin Injiniyar Jiragen Sama a sashen gyara na’urori. Daga 1983 zuwa 1986 kuma, ta koma karatu domin nazarin aikin babbar injiniyar jiragen sama da lantarki a Kwalejin Kere-kere ta Brunel da ke Bristol a Birtaniya, inda ta samu lasisin aiki daga Hukumar Jiragen Sama ta Birtaniya. A shekara ta 1990 ta samu digiri na biyu a fannin nazarin sarrafa kayayyaki mai zurfi daga Jami’ar Kingston.
Wannan kadan kenan daga Tarihin Injiniya Zainab kamar yadda muka nakalto daga kafar nazarin al’amuran mata na Sudan.