Wani rahoto mai taken “Zamanantarwa da Kasar Sin: Hanyar Ci Gaba,” wanda cibiyar bincike ta New China, ta kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da cibiyar nazarin tarihi da adabi na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) suka fitar, ya bayyana aikin zamantar da kasar Sin a matsayin wanda ya kawo sauyi ga kasar.
Rahoton wanda aka fitar jiya Asabar a birnin Paris na kasar Faransa, ya bayyana cewa, cikin gomman shekaru kadai a karkashin jagorancin JKS,Sinawa sun kammala aikin raya harkokin masana’antu, wanda ya dauki manyan kasashe daruruwan shekaru.
- Xi Jinping Ya Yi Jawabi Bayan Isa Kasar Faransa
- Shugaban Serbia: Kullum shugaba Xi Jinping Ya Cika Alkawarinsa
Ya ce kasar Sin ta samu dimbin nasarori a fannin zamanantar da kanta da cimma wasu abubuwan al’ajabi guda biyu, wato samun saurin ci gaban tattalin arziki da kyautatuwar zamantakewar al’umma mai dorewa.
Har ila yau, ya ce zuwa karshen 2020, an fitar da mutane miliyan 98.99 dake rayuwa cikin talauci a gundumomi 832 da kauyuka 128,000, daga kangin talauci.
A cewar rahoton, ta hanyar rage talauci, kasar Sin ta bayar da gagarumar gudunmuwa ga duniya, wanda ya dauki sama da kaso 70 na aikin yaki da talauci, haka kuma ya zama gagarumar nasara ga tarihin ci gaban bil Adama. (Fa’iza Mustapha)