Zambia ta kaddamar da sabon dakin taro na zamani da kasar Sin ta samar da kudin ginawa a jiya Talata.
An gina dakin taron na kasa da kasa da aka yi wa lakabi da The Kenneth Kaunda International Conference Center, domin karbar bakuncin taron tsakiyar shekara na Tarayyar Afrika (AU) da za a yi a bana. Babban dakin na da girman da zai iya daukar mutane 2,500.
Shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema, ya godewa kasar Sin da wannan gagarumar kyauta, yana cewa, gwamnatin na matukar godiya da taimakon da take bayarwa wajen raya ababen more rayuwa a kasar, wanda ta fara tun daga shekarun 1970, da ta gina layin dogon Tanzania zuwa Zambia (TAZARA).
A cewar shugaban, dakin taron zai bayar da gudunmuwa wajen mayar da Zambia cibiyar karbar bakuncin tarukan kasa da kasa. Ya kuma yabawa kamfanin kasar Sin da ya kammala aikin akan lokaci.
Du Xiaohui, jakadan Sin a Zambia, ya ce ginin alama ce dake nuna yadda dangantakar kasashen biyu ke kara kyautata. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp