Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa Jihar Zamfara na cin gajiyar tsananin hasken rana a duk shekara, inda ya sanya ta a matsayin wurin da ya dace da gonaki masu amfani da hasken rana da na’urorin samar da wutar lantarki masu zaman kansu.
Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara (REA) ta gudanar da taron tattaunawa da masana na jihar Zamfara a ranar Larabar da ta gabata a Abuja, inda ta tattaro masu ruwa da tsaki a fannin lantarki a ci gaba da tarukan dabarunta na jiha zuwa jiha.
- Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 50 A Benue
- Firaministan Sin Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen BRICS Na 17 A Brazil Da Kuma Ziyarar Aiki A Masar
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne kan farfaɗo da harkar wutar lantarki ta Zamfara, domin inganta zamantakewar al’umma, da ci gaba, da ƙirƙire-ƙirƙire ta hanyar samar da tsayayyen lantarki.
Sanarwar ta ƙara da cewa, a yayin taron an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Yankunan Karkara, sannan aka tattauna da masu ruwa da tsaki, tambayoyi da amsoshi, ra’ayoyi, da kuma alƙawura.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya ce ya gaji matalauciyar gwamnatin a bangaten lantarki.
Ya ci gaba da cewa, “An katse ƙananan hukumomi da yawa daga babban lantarkin ƙasa. An sace wayoyin lantarki da dama, wasu kuma sun lalace, wasu muhimman ababen more rayuwa sun durƙushe a cikin shekaru saboda watsi da su, sannan masana’antu da kasuwancinmu sun gurgunta saboda rashin ingantaccen wutar lantarki.
“Duk da haka, mun zaɓi kada mu shiga wasan zargi, a maimakon haka, mun mayar da martani ga ƙalubalen da muka gamu da su tare da hangen nesa mai muhimmanci, ƙuduri aiwatar da aiki da kuma yanke hukuncin cikin gaggawa.
“Tun daga wannan lokacin ne gwamnatinmu ta fara aikin sake rubuta wannan labari ta hanyar sanya hanyoyin samar da wutar lantarki a cikin dabarun ci gabanmu, mun ƙaddamar da ɗaya daga cikin shirye-shiryen samar da taransfoma na ƙasar nan, inda muka tura taransifoma sama da guda 150 a cikin birane da ƙauyuka.
“A tare da haɗin gwiwar Kamfanin Samar da Wutar Lantarki ta Kaduna mun maido da wutar lantarki a ƙananan hukumomi shida, kuma mun sake haxe wasu guda bakwai, waɗanda wasu daga cikinsu ba su da wutar lantarki sama da shekaru goma, wannan ƙoƙari na cikin wani shiri na zaburar da masana’antu, da kuma buɗe kasuwanni masu zaman kansu.
Gwamna Lawal ya ce, Zamfara tana ba da damammaki masu kyau don saka hannun jari a bangaren lantarki. “An albarkace mu da hasken rana mai tsananin ƙarfi a duk shekara, wanda ya sa mu zama wuri na farko da gonakin hasken rana za su samu habaka cikin sauri.
“Idan aka duba za a babban damar da madatsar ruwa ta Bakalori ke da shi, kadara ce ta samar da wutar lantarki da ba a yi amfani da ita ba, tare da yanki sama da hekta 30,000 na ban ruwa. Wannan haɗin gwiwa na hasken rana yana ba da damar ƙaddamar da hanyoyin samar da lantarki wanda zai iya ci gaba da ƙarfafa birane da karkara.
“Bangaren nomanmu wani muhimmin batu ne, a kullum jihar Zamfara tana cikin jerin manyan jihohin da ke girbin gero, dawa, waken soya, da gyaɗa a Nijeriya, muna sake fasalin wannan fanni ta hanyar ingantattun kayan aiki, injininan noma na zamani, da gyaran ban ruwa.
“Babban misalin sabunta kayan aikin mu shi ne filin jirgin sama na Gusau da filin jirageb ɗaukar kaya da ke kusa da shi, wanda aka tsara shi a matsayin ƙofa ga fasinjoji, kasuwanci da saka hannun jari.
“Don cimma burinmu na noma, muna nufin wannan ginin ya zama filin jirgin sama na farko a Nujeriya wanda zai samu wutar lantarki aƙalla kashi 50 cikin 100, kuma zai bai wa RESCO damar jagorantar sufurin jiragen sama mai ɗorewa.”
Tun da farko, Manajan Daraktan REA, Abba Abubakar Aliyu, ya tabbatar wa Gwamna Lawal ƙudirin hukumar na samar da kayayyakin wutar lantarki a jihar Zamfara.
“A karon farko a tarihin Nijeriya an yi taswirar ƙasar baki ɗaya, kuma hakan ya nuna adadin mutanen da ba su da wutar lantarki da kuma wurin da suke da shi, yanayin al’ummarsu da kuma buƙatar wutar lantarki, hakan ya taimaka wa RESCO da kuɗi, kuma gwamnatin jihar ta samu dabarar da za a bi don ganin cewa waɗannan mutanen sun samu wutar lantarki.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp