Sabon Darakta Janar na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Ahmed Musa, ya bayyana cewa samun mukamin shugabanci a ƙungiyar ba zai hana shi ci gaba da taka leda ba. A wata hira da yayi da RFI Hausa, Musa ya bayyana cewa kasancewarsa tsohon ɗan wasan Pillars tun lokacin ƙuruciya ne ya sanya zuciyarsa ke cike da ƙauna da kishin ƙungiyar. Ya ce yana jin ciwo idan ƙungiyar ta shiga halin rashin nasara, don haka zai ci gaba da bayar da gudunmawarsa.
Ahmed Musa ya kuma jaddada buƙatar samun cikakken goyon bayan magoya bayan Kano Pillars domin a samu damar farfaɗo da martabar ƙungiyar a fagen ƙwallon ƙafa. A cewarsa, ƙungiyar na buƙatar haɗin kai da jajircewar kowa domin samun nasara, musamman a wannan sabon zamani da ƙwallon ƙafa ke ƙara fuskantar ƙalubale.
- Ahmed Musa Ya Ƙaryata Kyautar Motoci Ga Ƴan Wasa Da Ma’aikatan Kano Pillars
- Makarantun Kano Za Su Fara Hutun Ƙarshen Zango A Ranar Juma’a – Gwamnati
A cikin kwanakin baya, Ahmed Musa ya jagoranci ƙulla yarjejeniya da RFI Hausa, wadda ya ce ita ce irinta ta farko da ƙungiyar ta taɓa samu tun kafuwarta. Yarjejeniyar ta kunshi samar da kayan wasanni da kuma kayayyakin aikin sada zumunta (Social Media), wanda zai ƙara inganta ayyukan ƙungiyar da kuma hulɗarta da duniya ta zamani.
Musa ya ce kasancewarsa a matsayin Manajan ƙungiyar ba zai hana shi taka leda ba idan buƙatar hakan ta taso. Ya bayyana cewa duk lokacin da ya ke wajen aiki, Ciyaman na ƙungiyar zai ci gaba da kula da duk wasu al’amuran ofishin ba tare da tangarɗa ba. Wannan, a cewarsa, zai tabbatar da cewa shugabancin ƙungiyar bai tsaya ga mutum ɗaya ba.
A ƙarshe, Ahmed Musa ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta ƙara zage damtse wajen tallafa wa ƙungiyar da kayan aiki da kuɗi. Ya ce burinsu shi ne su mayar da Pillars ƙungiyar da za a riƙa tsoro a gasar ƙwallon ƙafa a Nijeriya, kuma hakan zai yiwu ne kawai idan an samu cikakken tallafi daga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp