Gwamnan Jihar Bauchi kuma dan takarar Gwamnan Jihar a jam’iyyar PDP, Bala Muhammad ya ce a shirye yake ya karbi sakamakon zaben da ya zo ba tare da wata jayyaya ba.
Kazalika, gwamnan ya kuma gargadi jami’an rundunar sojin mayaqan sama da su daina shiga harkokin zaben a jihar.
- Makomata Na Hannun Allah, In Ji Gawuna Dan Takarar APC A Kano
- ‘Yansanda Sun Cafke Wakilan PDP 2 Suna Sayen Kuri’a A Ogun
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida bayan jefa kuri’a a rumfar zabe ta Bakin Dutse da ke Yelwan Duguri a karamar hukumar Alkaleri wajajen karfe 11:20 na safiya, Bala ya nuna damuwar kan yadda wata jirgi mai saukar ungulu ke shawagi a kauyukan da ke karamar hukumar Alkaleri ya na mai cewa sam bani adalci hakan.
“Na kai korafi wa shugaban kasa da sauran hukumomin tsaro kan cewa bana son jami’an hukumar sojin sama su tsoma mana baki a harkokin zabenmu saboda ina takara ne da tsohon hafsin mayakan sojin sama domin ba shi damar da ba ta dace ba.”
“A zahirin gaskiya ni a shirye na ke na amshi duk sakamakon zaben da ya zo mini, amma ba adalci ba ne jami’an sojin su na su zo kewaye mutane duk da kowa ya san suna bayan wani dan takara daya ne.”
Gwamnan ya yaba wa INEC bisa yin tsare-tsare masu kyau a yayin zaben da ke gudana. Ya nuna gamsuwarsa kan yadda aikin ke tafiya.
Ya kuma yaba da yadda mutane suka fito sosai domin kada kuri’a su. Ya kuka yi fatan a kammala zaben lafiya.