Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya ce wasu ‘yan siyasar da ke neman kujerar shugaban kasa a 2023 ba su da wata kyakyawar manufa face kawai muradin sace dukiyar Nijeriya.
Wike, ya ce wata rana a lokacin da ya dace zai fito ya shelanta wa ‘yan Nijeriya irin wadannan ‘yan siyasar domin al’ummar Nijeriya su yi watsi da su a zaben 2023.
- Gwamnatin Kogi Ta Haramta Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Bayan Rasuwar Mutane 2
- Yadda Bidiyon Tsiraicina Ya Karade Shafukan Sada Zumunta – Safara’u
Gwamna Wike, ya yi magana a jiya sa’ilin kaddamar da hanyoyi a Rumuesara, Eneka da ke karamar hukumar Obio/Akpor a jihar ta Ribas.
Ya ce, “Wasu sun dage kawai ta yadda za su karbi mulkin kasar domin sace sauran dan abin da sauran suka bari.
“Ni kam a lokacin da ya dace zan fada muku su waye wadannan mutanen. Akwai bukatar ku san mene ke faruwa a Nijeriya. Mance da dukkanin wanda ke yawo suna cewa suna son ceto Nijeriya ne. ku zura ido ku ga me zai faru nan gaba.
“Dukkaninmu mu kwantar da hankalinmu dangane da abin da ke faruwa a PDP. A zahiri ma, babu wani abun da ya faru zuwa yanzu. Da iznin Ubangiji, wani abun zai faru,” inji Wike.
Ya ce duk da kaddamar da kyawawan ayyukan raya Jihar Ribas da yake yi, amma wasu sun dauki nauyin bata masa suna a kafafen yada labarai.
Ya ba da tabbacin cewa irin wannan lamarin ba zai taba karkatar da hankalin gwamnatinsa daga shimfida kyawawan ayyukan raya jihar ba.