Jam’iyyun adawa a Nijeriya na wani shirin ƙarƙashin ƙasa don kawar da jam’iyyar APC mai mulki a kakar zaɓe me zuwa ta 2027.
Wanda muryarsa ta fi amo cikin masu wannan buri na ganin an yi haɗakar shi ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, wanda tun bayan da ya gaza kai labari a sakamakon ɓarakar da jam’iyyarsa ta PDP ta samu ya gano cewa lallai shi kaɗai ko PDP kaɗai ba za su iya kayar da APC.
- Obi Na Jam’iyyar Labour Ya Yi Wata Ganawar Sirri Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido
- 2027: PDP Za Ta Yanke Hukunci Kan Makomata — Atiku
Bayan haka Wazirin Adamawan Atiku Abubakar wanda ya yi wa jam’iyyar PDP takarar shugabancin ƙasa a zaben 2023, na da cikakkiyar masaniyar yadda haɗaka ke tasiri wajen yin nasarar zaɓe domin ita suka yi a baya suka kayar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.
Don haka ne ma bayan da suka kaye a hannun shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya duƙufa ainun wajen miƙa ƙoƙon barar a yi haɗaka tsakanin manyan jam’iyyun hamayya irinsu Labour (Party Peter Obi) da NNPP (Rabi’u Kwankwaso).
Ana kyautata zaton dai a kan wannan gaɓa ce ta haɗin kai Peter Obi ya kai wa Waziri Atiku ziyara, domin ya an jiyo Atikun yana cewa; “Ga duk wanda ya ke gani za a samu wani rikici tsakanina da Obi to babu abin da zai faru ko kadan, kuma mu a nan gaba kowa a dauko don ya yi takara in dai ya cancanta zamu goyi bayansa.”
Atikun dai ya bayyana cewa shi baya ƙin a samu shuagaban ƙasa daga kudu domin kuwa “Ai a baya na fada cewa idan jam’iyarmu zamu hadu ace a bar wa mutumin da ya fito daga Kudu maso Gabas zamu yar da.”
Wanda hakan ke nufin ko da Peter Obi PDP ta tsayar Atikun zai mara masa baya, sai kuma hakan da kamar wuya domin yanzu mulki na kudu nan gaba kenna Arewa zai dawo. Da kamar wuya a sake tsayar da ɗan kudun takara.
Yanzu dai tattaunawa ta fara ɗauka harama musamman tsakanin Labour Party da PDP sai dai har yanzu babu wani takamaiman bayani daga tsagin NNPP duk kuwa da a baya an ji yo Rabi’u Musa Kwankwaso yana cewa ƙofarsu a buɗe take don a kafa jam’iyyar haɗaka.
Daga cikin abin da zai ba wa PDP wahala shi ne shawo kan Kwankwaso ya yarda a haɗe da PDP, domin a burin Kwankwaso sai dai ko a dawo NNPP ko kuma a kafa sabuwar jam’iyya ba wai su sake komawa PDP ba.
Wazirin Adamawa din ya ce ba zai yi ritaya daga harkokin siyasa ba kuma za a ci gaba da dama wa da shi har sai lokacin da rai ya yi halinsa.
Batun takararsa kuwa Atiku Abubakar, ya ce,” A yanzu sai a saurara zuwa 2027 a gani ko zan tsaya takara ko kuma a’a.”