Ministar Tattalin Arzikin Kaifin Basira Da kirkire-kirkiren Nishadi, Hannatu Musawa a wata zantawa da ta yi da LEADERSHIP, ta bayyana ci gaban da ma’aikatarta ta samu tun bayan da ta dare kujerar minista da kuma kudirin da take da shi na samar wa gwamnatin tarayya kudin shiga da za su iya kai wa Dala Biliyan 100 a shekaru masu zuwa. RABILU SANUSI BENA ya fassara hirar kamar haka:
Tun daga lokacin da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu nada ki ministar ma’aikatar Tattalin Arzikin Kaifin Basira Da Kirkire-kirkiren Nishadi wane ci gaba kika samar?
Abubuwa da dama sun faru tun bayan da na zama ministar Tattalin Arzikin Kaifin Basira Da Kirkire-kirkiren Nishadi. Daya daga cikin abubuwan da ke nuna cewa Shugaba Tinubu ya damu da wannan fanni na fasaha da kirkire-kirkire shi ne, yadda ya jajirce wajen barin dogaro da hanyoyin samun kudaden shiga da muka saba gani, wato man fetur, kudin shige da fice, zirga-zirga da sauransu. Inda ya kirkiro wannan ma’aikatar ta fasaha, al’adu, da tattalin arzikin kirkire-kirkire irinsa na farko a tarihin Nijeriya.
Lokacin da na sami wannan aikin, na tarar cewar ba a shirya komai ba matukar ana son wannan jaririyar ma’aikatar ta samu abin da ake bukata, hakan ya sa na yi duk mai yiwuwa wajen ganin na tuntubi duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar fasaha da kirkire-kirkiren nishadi domin ganin an dama da su a wanna tafiyar kuma na samu hadin kan Shugaba Tinubu.
Na fito da ajandodi guda takwas da na mayar da hankalina a kansu, wadanda a nawa tunanin sune za su zama kamar wata matashiyar da za ta mayar da Nijeriya cibiyar kirkire-kirkiren fasaha da nishadi ta yadda za su samu damar samar da ayyukan yi ga dimbin matasanmu da ke da fasahohi daban-daban a fadin Nijeriya.
Kwanaki kin nuna cewa akwai wani shiri da kika yi a bangaren habbaka al’adun Nijeriya, ya maganar take a yanzu?
Wani muhimmin aiki da muke son maida hankali akai shi ne, habbaka kayan tarihi na al’adu a Nijeriya, wanda kuma daya daga cikin wajabcin ma’aikatar shi ne, muna fatan mayar da Nijeriya a matsayin cibiyar al’adun Afirka, musamman idan aka yi la’akari da nau’in bambancin kabilu da muke da su. Muna da babban shiri mai suna ‘Destination 2030’, wanda muka kaddamar a farkon shekara.
Shirin ‘Destination 2030’, wani shiri ne da muke so mu yi amfani da shi wajen sanya sunan Nijeriya a idon duniya. Mun kaddamar da shirin, kuma zai haifar da gagarumin sauyi ga yadda al’umar duniya suke kallon Nijeriya. Za mu mayar da wannan kasa tamu wani wuri da al’ummar duniya za su dinga sha’awar kawo ziyara da zuba hannayen jarinsu.
Ko akwai yiwuwar samar da wani matsuguni ga masu fasahar kirkire-kirkiren nishadi a Nijeriya?
Eh, muna da wannan buri na samar da kebabbun wurare da za mu dinga zakulo masu wannan fasaha da sauran fannoni a lunguna da sakon Nijeriya, domin yanzu haka mun tuntubi daya daga cikin wadannan matasa masu fasaha a Nijeriya, Mista Bayo, wanda shi ne mamallakin wani wurin nuna fasaha da ke Jihar Legas, kan yadda za mu bullo wa wannan lamari. Inda muke fatan samar da wadannan wurare a yankuna 6 da ke Nijeriya a matakin farko kafin daga bisani mu fadada shi zuwa kowace jiha.
Ko akwai abin da kuka shirya na ganin wannan shiri naku ya dore?
A matsayinmu na gwamnati, muna son duk abin da muka kawo wanda zai amfani kasa da al’ummar da ke cikinta ya zama ya dore, hakan ya sa muka tattauna da mutanen da ke da sha’awar taimakawa da shawarwari, kuma tuni muka fara tattaunawa kan yadda za mu samar da katafaren filin wasa guda daya a tsakiyar Abuja. Sannan muna fatan samun abin da muke kira ‘Abuja Creatibe City’, wanda zai zama wurin tsayawa ga duk wani abu da yake da fasahar kirkire-kirkire a Nijeriya.
Ya maganar samar wa matasa ayyukan yi kamar Yadda kika alkawaranta a kwanakin baya?
Idan ana maganar samar da ayyukan yi, wanda yana daya daga cikin abubuwan da muka himmatu a matsayinmu na ma’aikata, don haka matasa za mu iya samar musu da ayyukan yi ko a gida Nijeriya ko a fadin duniya. Muna aiki don ganin hakan ta tabbata.
Kin yi magana game da samar wa gwamnatin tarayya Dala Biliyan 100 nan da shekarar 2030, ta yaya za a cimma hakan?
Hakan zai iya yiwuwa idan aka yi la’akari da dimbin dukiyar da ake samu a wannan fanni na nishadi da fasahar kirkire-kirkire na manyan kamfanonin kasashen waje irinsu ‘Spotify, YouTube’, da ‘NETFLID’ suna bayar da kudi idan aka yi abin da ya dace. Zan so ku yi la’akari da babban fim din Funke Akindele, wanda ya samu biliyoyin nairori a lokacin da ya fitar da fim dinsa a silima.
Masana’antar fina-finai ta Nijeriya ita ce ta biyu mafi girma a duniya, amma ba su da kayan aiki da kuma goyon bayan da ya dace don samun damar samar da kyawawan fina-finai. Manyan masana’antun shirya fina-finai a duniya irinsu ‘Bollywood’ da ‘Hollywood’ suna samun biliyoyin daloli ta sanadiyar shirya ingattattun fina-finai, bayan harkar fim akwai manyan masana’antu a Nijeriya kamar masana’antar kayan kwalliya, masana’antar kida da masana’antar dafa abinci.
Hakan ya sa muke ganin idan aka gyara wadanna masana’antun aka yi duk abin da ya dace zuwa ‘yan shekaru nan gaba za mu iya samar wa gwamnatin tarayya adadin kudin shiga kimanin dala biliyan 100 ta hanyar fasahohi da kirkire-kirkiren nishadi.