Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana cewa, ya yi alkawarin tabbatar da aniyar ganin ana tafiyar da ayyuka a daidai a Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a Afrika ta Yamma.
Dantsoho wanda kuma shi ne, Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Kula da Harkar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Afrika ta Yamma wato IAPH ya sanar da cewa, hakan zai taimaka, wajen magance kalubalen da Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a yankin, ke fuskanta.
- Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja
- 2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara
Kazalika, ya ce, NPA na ci gaba da yin kokari wajen sama da saukin wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci ta hanyar Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, wanda hakan ya sanya, har manyan Jiregen Ruwa suka fara shigo da manyan Kwantainoni zuwa cikin Tashoshin.
Dantsoho ya sanar da haka ne, bayan kaddamar dashi a matsayin Mataimakin Shugaban Kungiyar a kwanan baya a wani taro kan harkokin Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya da aka gudanar.
Kazalika, Dantsoho ya ci gaba da cewa, zai mayar da hankali ne, kan wanzar da tsarin da NPA, ta sanya a gaba da kara karfafa hadaka, musaman domin a habaka samar da sauki a fannin gudanar da hada-hadar Tashohin Jiragen Ruwa da ke a Afrika ta Yamma.
Idan za a iya tunawa, harkar gudanar da Tashoshin Jiragen Ruwa na Afrika ta Yamma na fuskantar kalubale da suka hada da, yin aiki da kayan da suka dade da rashin samar da dawamammen tsari da kuma rashin rungumar yin aiki da kayan aiki na zamani.
Sai dai, ya sanar da cewa, ta hanyarin amfani da kayan aikin zamani, hakan zai bai wa Hukumarsa damar kara samun masu zuba hannun jari a fannin.
“Wannan nuyin da aka dora min, zai kara bani wata damar ta kara yin aiki tukuru wajen daukar matakan kara saita ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa da a yankin na Afirka ta Yamma tare da kuma kara habaka tattalin arziki, “Inji Shugaban.
Ya kuma nanata cewa, zai tattabatar da ya joranci ganin ana yin amfani da fasahar zamani, musamman domin a kawar duk wani shinge na hada-hadar kasuwanci da zai haifar da wani jinkiri.