Hon. Keftin Amuga, shaharraen dan siyasa ne tun a zamanin jamhoriya ta biyu, kuma kwararre ne a fagen tafiyar da harkokin al’umma shi ne kuma Wakilin Tagale kuma dan takarar neman kujerar gwamnan Jihar Gombe a karkashin jam’iyyar Labour Party (LP), a tattaunawarsa da Mataimakin Editanmu Bello Hamza, ya yi ciakken bayanin yadda zai samar da zama lafiya da bunkasar tattalin arzikin Jihar Gombe tare da tabbatar da adalci.
Ranka ya dade, ko zo ka gabatar mana da kanka
Suna na Hon. Keftin Amoka.
Zamu so mu ji takaitaccen tarihin ka
Ni dai daga Gombe neke, ni kuma Wakilin Tangale a majalisar Jihar Bauchi daga 1979 zuwa 1983. A karkashin jam’iyya Nigeria People’s party (NPN). Ni dai a zamanin mun yi aiki bisa sahihiyar siyasa ba ma siyasar kudi. A lokacin an tabbatar da ayyuka wanda na yi da suka hada da ‘Federal Gobernment College Gardin Sarki. Lokacin Hakimi ne aka bashi sanda tun zamanin, mun samar da su Nitel, Rijiyoyin Burtsatse da sauran ayyukan more rayuwa ga al’umm. A ilmance kuma na yi karatun sakandare a ‘Gobernment College Kaduna’ daga 1968 zuwa 1972. Na tafi ABU Zaria (SBS) 1973 zuwa 1977. Daga nan na tafi NYSC a Jihar Ondo. Na dawo na kama aiki a Jihar Bauchi. Toh daga nan sai na amshi kiran mutanen mu a kan in zo in tsaya a don wakiltarsu a majalisa.
Ranka ya dade ganin cewa kana daya daga cikin ‘yan Takaran Gwamna a Jihar Gombe karkashin Jamiyyar LP wato Labour Party me ka tanadar wa al’ummar Jihar Gombe in ka kai ga nasara?
Na farko shi ne tabbatar da zaman lafiya da daidaita zamantakewar al’umma. Domin in babu zaman lafiya a cikin rayuwar mutane, cigaba da bunkasar kasa ba zai samu ba. Zaman lafiya na da matukar muhimmanci. Domin wannan duk wani abu na ganganci ko na Gwamna wanda zai kawo wariya ya kuma daga hankali a cikin al’umma ba zan yarda dashi ba. Zan kauda shi. Ka ji dai bayanin da na yi a kan maganan Sabon Sarkin Tanga. Gwamnati ta bada umurnin aje a yi zabe majalisa sarakuna suka yi zabe wanda suka sa a gaba shi ne Dakta Musa Idris ya samu kuri’a biyar a ciin kuri’a tara na ‘yan majalisa. Suaran biyu suka samu kuri’a biyu. Bisa ga al’ada kuma yadda aka saba yi. Duk wani wanda ya samu kuri’a mafi tsoka fiye da sauran shi ne ake nadawa. Amma a wannan lokacin da aka turo rahoto sai gwamnati ta dauki sarauta ta ba wanda ya samu kuri’a biyu. Don mene ne haka ya faru? Saboda haka mu maganar bamu taba sanin cewa maganan addini zai raba mu ba. Toh irin wannan abubuwan ba zamu yarda da su ba . Ba zamu yarda ba. Kuma koda na zama gwamna irin wannan halaye na ganganci na rashin gaskiya zamu kawar da su don samar da adalci a tsakanin al’umma.
Ranka ya dade ganin cewa matasa su ne kashin bayan al’umma mene ne gwamnatin ka za ta tanadar musu don rage zaman kashe wando a tsakanin al’umma
Toh ni ko da na tashi ina yaro ban ga matasa suna zama gindin itace ba, ba za ka taba ganin yara suna zama gindin itace ba. Domin me? Domin iyaye ba za su yarda ba. Abin da yake faruwar yanzu da ‘ya’yan mu ba daga sama suka sauko ba suna da iyaye. Mu iyaye mun gaza a cikin aikin kula da yayanmu kamar yadda kakanninmu iyayenmu suka yi mana. A zamanin mu yaushe zaka tsaya kana shan sigari a gaban iyayen ka ko giya, ko kuma kana wucewa da yarinyar ka a gaban iyaye. Amma yanzu zaka ga yara suna yin abin da bai kamata ba amma Iyayen na kallo. To zamu fara daga kan iyayen ne tukun. Mu tabbata kowa yasan. alhakin da ke kansa kafin muje mu tabbatar cewa masu siyar masu da kwayan nan su burtutu dinan zamu tattauna dasu, yaya suke so maganan rayuwa ne? Wannan batu da kyau za mu tattauna da wadannan abubuwan domin akwai illa da yawa akai sannan zamu tambaye su wace sana’a da suke so suyi sai mu taimaka masu.
Wato ranka ya dade mene ne gwamnatin ka ta tanada don bunkasa noma da kiwo wandada sune manyan sana’o’in al’ummar jihar Gombe dama Nijeriya ma baki daya?
Noma shi ne tushen arziki. Saboda haka za mu inganta shi. Za mu inganta shi, kasan duk arzikin Amurka noma ne mu kuma na tabbata kasar Amurka bata fi ni’imar kasar mu ba. Toh tunda yake jama’a sun yarda sun karbi sana’ar nan suna yi kowane lokaci ba a sa su tilas dole ne su yi domin su samu su ciyar ma kansu. Gwamnati za ta shiga ta tallafa masu. Tallafi a kowani lokaci a lokacin da yakamata in taki ne, in maganin feshi, in mene duk wani abunda gwamnati za ta zuba. Gwamnati na za ta zuba a yi taimako a cikin wannan.
Toh ranka ya dade ganin cewa zaku fuskanci jam’iyya mai mulki ya kake ganin zaku wani hanya kuke ganin za ku lashe wannan zaben ganin cewa su suna rike da mulki yanzu.
Na farko kam wannan jam’iyya masu mulki suna mana yakin neman zabe ne da kansu ta hanyatr a ayyukan su da maganganun su suna taimaka mana a yakin meman zabe. Amma duk wanda suke in kaga mutum wanda ya ce zai yi PDP zai dauki kuria’ar sa ya ba da takarar gwamnan APC Toh bai yi da gaskiya Toh mu mun dogara ga Allah kuma muna gani a ayyukan da wadannan manyan jam’iyyun suke yi. A na uku jama’a sun na ji a jikin sun. Sun dandana kuma suna ganin sun yadda yanzu mun yi laifi. Mun yi kuskure da muka zabi wannan guda biyu. Toh ba kudi muke da shi ba. Wani kudi muke dashi? Baza mu taba yarda mu kawo maganar kudi ba domin suna da gwamnati amma ayyukan su da abin da mutane suka wahalar da mutane suka ji a jikin su su ne ‘Campaign a gare mu. Shi zai jawo mana mutane.
Toh ranka ya dade zuwa yanzu ka gamsu da yadda hukumar zabe na INEC ke gudanar da ayyukan ta?
Toh yanzu da maganar zabe kam, Kamar yadda ya faru a Jihar Osun dinnan ta hanyar amfani da na’ura mai kkwakwalwa yanzu babu maganar sace akwati. Babu maganar rubuta sakamakon zaben da ba a yi, ko kuma dangwala kuri’a fiye da daya. Toh tun da yake INEC ina ganin ya kai sau biyu ko sau uku ana sa masu matsa lamba suna kokarin ganin an tabbatar da yin zabe sahihi bay tare da magudi bapressure suyi kokari su koma ga hanyar zabe na kwanan baya. Toh sun yi resisting sun ce ba za su yi ba. Toh sai muce at this point Alhamdulillahi. Shirye-shirye da abun da ake ciki yanzu zai biya bukata a kasar nan baki daya.
Ranka ya dade wani kira kake dashi na musamman ga magoya bayan ka a daidai wannan lokaci?
Muna cikin yaki zaben nan. Wannan zaben 2023 ba kamar zaben da ya wuce ba. Zabe ne na tabbatar da makomar al’umma da kuma kasar Nijeriya. Magoya baya na in akwai abin da yafi komai a duniya tsoro ban tsoro shi ne maganan zaben nan mai zuwa. Ya kamata a nats a yi mai tsafta cikin kwanciyar hankali.
Ranka ya dade daga karshe ko akwai wani bayani da kake so ka yi wa al’umma wanda zuwa yanzu ban tambaye ba?
Bayani na mai sauki ne yakamata ‘an arewa su kawar da banbancin addini da kabilanci don a samu cikakkemn cigaba a dukkan bangarorin rayuiwar al’umma
Ranka ya dade muna godiya
Na gode