Wasu ɓata-gari a yayin zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa da ake ci gaba da yi a ranar Alhamis a kasar nan, sun bankawa wani bangare na ofishin Hukumar Kula da Dokokin Sufuri ta Jihar Kaduna (KASTLEA) wuta tare da kwashe wasu kadarori na hukumar.
Sun kuma lalata wani bangaren ginin hedikwatar hukumar bunkasa zuba jari ta Kaduna (KADIPA), da ke makwabtaka da ginin na KASTLEA.
- Bata-gari Sun Cinna Wa Sabon Ofishin NCC Wuta A Kano
- Masu Zanga-Zanga Sun Toshe Hanyar Abuja Zuwa Keffi
Wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya ce, ɓata-garin sun kuma kara yin awon gaba da wasu kayayyakin amfani a gidan wani jami’in soji.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, harin da aka kai kan ofisoshin gwamnati, na faruwa ne a daidai lokacin da masu zanga-zangar #EndBadGovernance suka fito kan tituna domin nuna adawa da kuncin rayuwa da yunwa a kasar.
Mai taimaka wa Gwamna Uba Sani kan kafafen sadarwa na zamani, Abdalla Yunus, ya tabbatar da wawashe da barnata kadarorin gwamnati yayin da yake mayar da martani kan lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp