Majalisar dattawa ta bukaci masu da’awar zanga-zanga a fadin Nijeriya da su dakatar da shirye-shiryensu domin ci gaban kasa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya yi wannan rokon bayan wani zaman gaggawa da Sanatocin suka yi a Abuja, ranar Laraba.
- Zaben Kananan Hukumomi: Za A Yi Wa ‘Yan Takara Gwajin Kwaya A Kano
- Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Jirgin Arik Daga Yin Jigilar Fasinjoji Saboda Bashi
A ‘yan kwanakin nan ne, wasu matasa a kasar suka yi kira ga al’ummar Nijeriya da a tsunduma zanga-zanga a fadin kasar daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga watan Agusta, biyo bayan tsadar rayuwa a kasar.
Akpabio ya ce, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu shekara guda kacal ta yi, amma ta bullo da tsare-tsare da za su amfani ‘yan Nijeriya nan gaba kadan, don haka, ya dace a kara hakuri.