A yau Litinin mazauna birnin Legas a Nijeriya, suka fito kan tituna don nuna rashin gamsuwarsu kan halin tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da ke addabar kasar.
LEADERSHIP HAUSA ta samu labarin cewa wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai suna ‘Take It Back Movement’ ce take gudanar da zanga-zangar da ake yi yanzu haka a Legas.
Masu zanga-zangar dauke da kwalaye da rubuce-rubuce daban-daban, wadanda ke bayyana kokensu, sun zanga-zangar sun fito sun yi cincirindo a kasan gadar unguwar Ojuelegba a Legas.
Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan gabanin gudanar da zanga-zangar da kungiyar kwadago a Nijeriya (NLC) ke shirya gudanarwa a duk fadin kasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu kan tsadar rayuwa.