Gwamnatin jihar Yobe ta sanya dokar hana zirga-zirga ta sa’o’i 24 a yankunan Potiskum, Gashua da Nguru na jihar bayan da wasu bata-gari suka mamaye zanga-zangar tare da wawure kadarorin gwamnati.
Mai bawa gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro, Brig. Janar Dahiru Abdussallam (mai ritaya), a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis ya ce, dokar ta fara aiki nan take.
“Gwamnatin jihar Yobe ta yi la’akari da yanayin tsaro a garuruwan Potiskum, Gashua, da Nguru, inda wasu bata-gari suka fara lalata dukiyoyin jama’a da barnata kadarorin gwamnati” in ji sanarwar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp