Duk harkokin kasuwanci sun tsaya cak na wani dan lokaci a Benin, babban birnin jihar Edo a ranar Litinin bayan wata zanga-zangar da kungiyoyin farar hula ta Edo (EDOCSO) suka gudanar, suna kira ga shugaba Bola Tinubu da ya magance matsalar yunwa a Nijeriya ko kuma ya yi murabus.
Kungiyar wadda ta gudanar da zanga-zangar tun daga titin Ring Road zuwa titin Akpakpava da sauran manyan tituna a tsakiyar birnin, sun buga tamburan kiraye-kiraye daban-daban kamar su “’yan Nijeriya na fama da yunwa”, “Tinubu, ka kawo karshen yunwa da wahala a Nijeriya”, “Tinubu, bari ‘yan Nijeriya su numfasa” da dai sauransu.
In ba a manta ba, a baya kungiyar ta baiwa shugaba Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wa’adin kwanaki 14 da su yi murabus ko kuma su yi gaggawar gyara tattalin arzikin Nijeriya.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na rikon kwarya, Austine Enabulele, wacce aka rabawa manema labarai a Benin a lokacin zanga-zangar.