• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zarge-zargen Shugaban Sojin Nijar Kan Nijeriya Ba Su Da Tushe – Gwamnatin Tarayya

by Sulaiman
10 months ago
Nijar

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaryata zargin da Shugaban Sojin ƙasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo, inda ya zargi Nijeriya da haɗa kai da Faransa domin tayar da zaune tsaye a ƙasar sa.  

A cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya fitar a ranar Alhamis, gwamnati ta bayyana zargin a matsayin “mara tushe kuma wanda aka ƙirƙira kawai.”

  • Ƙasa Da Sa’o’i 30 Da Rasuwar Mahaifiyarsa, Gwamnan Jigawa Ya Sake Rasa Ɗansa A Hatsarin Mota 
  • Sin Ta Gabatar Da Rukuni 2 Na Kayayyakin Agajin Gaggawa Ga Al’ummun Gaza Ta Mashigin Kasar Masar

“Nijeriya ba ta taɓa shiga wata yarjejeniya ta ɓoye ko ta fili da Faransa—ko wata ƙasa—ba domin ɗaukar nauyin hare-haren ta’addanci ko tayar da zaune tsaye a Jamhuriyar Nijar,” inji Idris.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Ministan ya jaddada cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a matsayin sa na Shugaban Ƙungiyar Haɗa Kan Yankin Afrika ta Yamma (ECOWAS), ya nuna bajinta ta shugabanci, inda ya ci gaba da buɗe ƙofa ta diflomasiyya da Nijar duk da rikicin siyasa da ake fuskanta a ƙasar.

Idris ya tabbatar da cewa Nijeriya za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai da kyakkyawar alaƙa da Nijar.

Haka kuma ya musanta zargin cewa Nijeriya tana yunƙurin lalata bututun mai da harkar noman Nijar, ya kira wannan zargin “mara tushe kuma mai cutarwa.”

Ya ce Nijeriya ta daɗe tana taimaka wa bunƙasar tattalin arzikin Nijar ta hanyar manyan ayyuka na haɗin gwiwa kamar bututun iskar gas da ya ratsa Sahara da kuma layin dogo na Kano zuwa Maraɗi.

Nijeriya ta kuma ƙaryata iƙirarin cewa wai an kafa wata hedikwatar ta’addanci ta Lakurawa a Jihar Sakkwato tare da haɗin baki tsakanin Nijeriya da Faransa.

Idris ya musanta wannan batu, yana mai bayyana jagorancin da Nijeriya ke yi wajen yaƙar ta’addanci a yankin, ciki har da shirin nan na ‘Operation Forest Sanity III’ wanda aka ƙaddamar kwanan nan.

“Ta yaya za a zargi gwamnatin da ke ƙoƙarin yaƙar barazanar Lakurawa da ɓoye ƙungiyar a cikin ƙasar ta?” inji Idris, yana mai bayyana zargin a matsayin mara gamsasshiyar hujja da kuma wani ƙoƙari na karkatar da hankali daga matsalolin cikin gida da Nijar ke fuskanta.

Ministan ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan ƙarairayi, yana ƙalubalantar Tchiani da ya gabatar da hujjoji masu ƙarfi don tabbatar da zarge-zargen sa.

Ya bayyana duk wani yunƙuri na yi wa Nijeriya barazana kan matsayar ECOWAS na adawa da karɓar mulki ba bisa doka ba da aka yi a Nijar a matsayin “mai cike da yaudara kuma wanda ba zai cimma nasara ba.”

“Nijeriya za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a yankin tare da jagorantar ƙoƙarin magance matsalolin ta’addanci da sauran ƙalubale na ƙetare,” inji Idris.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Asuu
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro
Labarai

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
majalisar kasa
Labarai

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
Next Post
Sin Ta Bayyana Sakamakon Kidayar Harkokin Tattalin Arziki Karo Na 5

Sin Ta Bayyana Sakamakon Kidayar Harkokin Tattalin Arziki Karo Na 5

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.