Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf, tsohon babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS) a gaban babbar kotun birnin tarayya (FCT) da ke Kuje bisa zargin zamba, almubazzaranci, da kuma almundahanar Naira miliyan 90.4.
Daya daga cikin tuhume-tuhumen da ake masa shi ne zarginsa da amincewa da sayen mota a kan Naira miliyan 49.1, wanda ya zarce Naira miliyan 30 da aka ware masa, yayin da wani kuma ya ce ya bayar da kwangilar Naira miliyan 10.1 ga wata gidauniyar da ke bada kudin ruwa.
Mai shari’a Chinyere E. Nwecheonwu ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairun 2025, domin sauraren karar beli da aka nema, sannan ta bayar da umarnin a tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har sai an saurari karar.