Majalisar dokokin jihar kaduna ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi Uku kan zargin badakalar kudade.
Ta dakatar da su ne a ranar Talata bisa zargin su da bayar da kwangila ba bisa bin ka’idar dokar jihar ba ta bayar da kwangila ta shekarar 2016 da aka sabunta wacce ta yi dai-dai da sashe na 35 da sashe na 23 na kundin dokar.
Majalisar ta dauki matakinne a zamanta na ranar Talata bayan gabatar da rahoton kwamatin binciken harkokin kudade na kananan hukumomi biyar na jihar wacce shugabar kwamitin, ‘yar majalisa mai wakiltar mazabar Lere, Munirat Tanimu suleman ta jagoranta.
Munirat ta ce, kwamitin ya bukaci shugabannin kananan hukumomin da su bayar da takardun kudaden da suka kashe daga cikin kasafin kudaden da aka amince musu daga watan Yunin 2022 zuwa watan Yunin 2023 da kuma rahoton kwangilolin da suka bayar da sauran batutuwan kudi da suka shafi kananan hukumomin.
Bayan kwamitin ya yi nazari kan takardun, ya gano cewa, shugabanin na kananan hukumomin Kaura, Kagarko da Chikun, sun sabawa sashe na 48 na dokar 2018 da kuma sashe na 35 da sashe na 25 na dokar jihar Kaduna wacce aka tanada kan bayar da kwangila.
Don haka, Kwamitin ya bayar da shawarar dakatar da shugabannin har tsawon watanni shida don samun damar gudanar da cikakken bincike akansu.