Tsohuwar ministar jin kai ta Nijeriya Sadiya Umar Farouq ta kai kanta ofishin Hukumar EFCC da ke Abuja domin amsa tambayoyi game da badaƙalar N37b da ake zarginta da karkatarwa tare da wani dan kwangila James Okwete.
Sadiya Umar din ce ta bayyana hakan a shafinta na twitter a ranar Litinin.
- Tsohuwar Ministar Ayyukan Jin-Kai Ta Ki Amsa Gayyatar EFCC
- Tsohuwar Ministar Jin Kai, Sadiya Ba Ta Ƙi Amsa Gayyatarmu Ba – EFCC
Ta ce ” Yau na je Hedikwatar Hukumar EFCC domin amsa gayyatar da suka yi min da kuma amsa tambayoyin su kan wani bincike da suke gudanarwa”.
Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne Hukumar ta gayyaci Sadiya, sai dai kuma ba ta samu zuwa ba saboda wasu dalilai na rashin lafiya da ta ba wa Hukumar.