Majalisar dokokin Jihar Kaduna ta ce ta tsaya kan rahotonta na tuhumar tsohon gwamna jihar, Nasir El-Rufai kan zargin karkatar da naira biliyan 423, 115,028,072.88.
A cewar majalisar, wasu tsirarun masu rike da mukaman siyasa a tsohuwar gwamnatin Jihar Kaduna da suka yi magana da manema labarai a Abuja, sun yi ta yin maganganu na boye gaskiyar lamari, amma yunkurin tozarta majalisar da kuma boye zamba da ake zargin gwamnatin el-Rufa’i da tafkawa ba su wakilci kowa ba face su kansu.
- Yadda Ministan Yaɗa Labarai Ya Karɓi Baƙuncin ‘Yan Jaridar Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
- Ƴan Ta’adda 284 Sun Miƙa Wuya Ga Sojojin Haɗaka
Majalisar ta ce, “Idan da gaske suna da kishin Jihar Kaduna me zai hana sun dukufa wajen neman hanyar ci gaban jihar a maimakon shiga cikin zargin satar dukiyar da ke cikinta.”
Shugaban kwamitin binciken kuma mataimakin kakakin majalisar, Henry Magaji a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, “An jawo hankalin majalisar dokokin Jihar Kaduna kan taron manema labarai da wasu manyan masu rike da mukamai na siyasa na tsohuwar gwamnatin da ta shude suka yi jawabi kan el-Rufai.
“A cikin taron manema labarai, tsoffin masu rike da mukaman siyasa sun yi matukar kokari wajen ganin sun samu wata kafa a cikin rahoton kwamitin binciken. Sun koma ta yin kiraye-kirayen kan zarge-zargen wannan binciken na majalisa. Muna so mu bayyana abubuwa kamar haka:
“Taron ‘yan jarida da suka yi, wani sabon salo ne na zage-zage da batanci da tsofaffin masu rike da mukaman siyasa suka yi mana a taron manema labarai da suka yi a Abuja. Babu wani abu da zai sa mu mayar da martani. Sun kasa magance al’amarin, wanda shi ne tsare-tsare da hadin gwiwa na karkatar da dukiyar al’ummar Jihar Kaduna ta hanyar bayar da kwangilolin da ba su dace ba.”