Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi murabus daga mukaminsa na Alkalin Alkalan Nijeriya (CJN).
Rahotanni sun bayyana cewa ya mika takardar murabus dinsa ne a wata wasika da ya aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa dalilansa cewa yana fama da rashin lafiya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu alkalan kotun ke Zargin alkalin alkalan da cin hanci da rashawa.
A wata takardar koke mai dauke da sa hannun alkalan kotun koli 14, sun zargi Muhammad da kin ba su hakkokinsu Wanda doka ta tanadar musu.
Alkalan sun ce, horon da suke samu na shekara-shekara a kasashen waje, da nufin bunkasa karfin tsarin shari’ar kasar, Muhammad ya hana su.
Daily trust ta nakalto cewa, daga cikin manyan koken alkalan da suka gabatar a cikin wasikar da suka mika wa kwamitin jin dadin alkalan sun hada da; rashin saya musu sabbin motoci; ba suda kyawawan masaukai; rashin magunguna a asibitin Kotun Koli; karancin wutar lantarki a Kotun Koli; wutar lantarki ta yi tsada; babu karin Kudi akan kudin alawus na Siyan man Jannareta; babu yanar gizo a dakunan su da ofisoshinsu.