A ranar Litinin din nan ne jam’iyyar Action Peoples Party (APP) za ta maka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu kara domin kalubalantar cancantarsa ta neman tsayawa takara a zaben 2023.
Matakin dai ya biyo bayan wasu kura-kurai aka samu a takardun makarantun da ake zargin Tinubu ya aike ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
- Zaben Fidda-Gwanin APC: A. A Jinjiri Ya Maka Bashir Machina Kotu
- Sha’aban Sharada Ya Maka Dan Takarar Gwamnan APC Na Kano A Kotu
Shugaban jam’iyyar, Uche Nnadi ne, ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya kara da cewa jam’iyyar na da isassun hujjoji.
A cewar Nnadi, buga jerin sunayen ‘yan takarar da INEC ta fitar, ya nuna cewa dan takarar APC, Tinubu bai cancanci tsayawa takara ba saboda fom dinsa na dauke da bayanan karya.
Ya ce; “Tinubu ya musanta halartar firamare da sakandare amma ya yi ikirarin yin digiri a jami’a a sabon fom din da INEC ta buga yau.
“Tinubu ya yi rantsuwar inda ya ce ya yi makarantar firamare a baya, ya yi rantsuwar lokacin tsayawa takarar gwamnan jihar Legas, amma yanzu ya yi ikirarin cewa bai yi makarantar firamare ba. Abin da ke kunshe a fom din Tinubu ya saba wa rantsuwar da ya yi a shekarar 2007 cewa ya halarci makarantar firamare da sakandare.”