Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule-Garo da ‘yan uwansa biyu, Mustapha Sule-Garo da Mohammed Sule-Garo kan zargin karkatar da kudaden kananan hukumomi har Naira biliyan 2.8.
A karar da babban lauyan gwamnatin jihar kuma kwamishinan shari’a ya shigar, ta hannun lauyansa, Auwal AbdulQadir-Sani, ya zargi wanda ake tuhuma da amfani da kudaden wajen siyan kadarori a kasar Saudiyya.
- Gwamnatin Kano Ta Gabatar Da Sabbin Tuhume-tuhume Kan Ganduje Da Kwamishinansa
- Matsalar Karancin Abinci Za Ta Ƙare Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamnatin Tarayya
A bisa tuhume-tuhume da aka shigar a babbar kotun jihar Kano, gwamnatin jihar ta yi zargin cewa, an karkatar da kudaden ne daga asusun gudanar da kananan hukumomi da kuma kashi daya bisa dari na kudaden bayar da horo.
Auwal ya ce, an shigar da karar ne a karkashin sashe na 211 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima da kuma sashe na 121 [1], 123 [1] [a], 126 [b], da 377 na dokar shari’a ta jihar Kano [2019].
Mutane bakwai ne ake tuhuma a karar da suka hada da tsohon kwamishinan da ‘yan uwansa biyu da wani ma’aikacin ma’aikatar kananan hukumomi da kamfanoni biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp