Fadar Shugaban Kasar Nijeriya, ta yi watsi da rahoton baya-bayan nan da kwamitin hulda da kasashen wajen Amurka ya fitar, wanda ya kafa hujja da amincewar majalisar dokokin kasar, na zargin kakaba wa wasu kiristoci takunkumi a kasar.
Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Daniel Bwala, ya bayyana rahoton a matsayin wanda ba shi da tushe da makama, yana mai jaddada cewa; tun bayan lokacin da Shugaba Tinubu ya dare kan kujerar mulki a ranar 29 ga Mayun 2023, al’amuran cin zarafi, musamman ta fuskar addini suka yi matukar ja da baya.
- Sin: Shingayen Kasuwanci Suna Illata Wadatar Tattalin Arzikin Duniya
- Wa Ke Dandana Kudar Matakin Harajin Kwastan Da Gwamnatin Amurka Ta Dauka
Bwala, ya yi wannan furuci ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, wato na D; yana mai jaddada cewa, gwamnatinsu mai ci yanzu; ta himmatu wajen kokarin daidaita addinai a matsayin abu guda.
“Gwamnatin Bola Tinubu, koda-yaushe na kokarin bai wa addinai muhimmanci na musamman. Tun daga ranar 29 ga Mayun 2023, daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau kan karagar mulki, ba a taba samun wasu matsaloli na tsananta wa Kiristoci a ko’ina a fadin wannan kasa ba”, kamar yadda ya rubuta.
Ya jaddada cewa, Nijeriya ta kasance kasa mai dauke da addinai daban-daban, sannan a kowane lokaci gwamnati na kokarin samar da zaman lafiya a tsakanin wadannan addinai.
Martanin da Fadar Shugaban Kasar ta mayar, ya biyo bayan nuna damuwa a kan matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na amincewa da takunkumin da aka kakaba wa Nijeriya, bisa zargin kashe Kiristoci.
Da yake goyan bayan wannan matsaya, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen Arewa, Rabaran Yakubu Pam ya bayyana a baya bayan nan cewa, abubuwan da suke faruwa na musgunawa Kiristoci, su yi matukar raguwa.
Har ila yau, ya bayyana ci gaban da aka samu, musamman a bangaren wariya ko nuna banbanci ga Kiristoci, wajen mallakar filaye; domin gina Coci-coci da kuma batun tilasta barin addinin da kuma aurar da yara ‘yan mata Kiristoci.
Kazalika, gwamnati ta sake nanata kudirinta na ci gaba da karfafa addinai tare da ba su muhimmanci, inda kuma ta bukaci kungiyoyin kasa da kasa da su yi la’akari da abubuwan da suke faruwa yanzu, maimakon rika dogaro da rahotannin da suka riga suka gabata.
Haka zalika, wata sanarwa da mukaddashin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ta sanar da LEADERSHIP; ta bayyana damuwarta kan yadda ake faman yada labaran karya da kuma rahotannin bata-gari, dangane da kashe-kashen da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya.
“Wadannan rahotannin karya da shaci fadi, na ci gaba da yin tasiri ga gwamnatocin kasashen waje, musamman ma Gwamnatin Amurka; don ayyana Nijeriya a matsayin kasa mai cin zarafin Kiristoci.
Don haka, Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar, ta bukaci kasashen duniya da su yi taka-tsan-tsan tare da rika tantance bayanai, kafin su kai ga yanke hukunci ko yin kalaman da ka iya tayar da rikici a Nijeriya. “Muna kira ga masu ruwa da tsaki, ciki har da kafafen yada labarai, kungiyin al’umma da kuma abokan huldar kasashen waje; su guji yada labaran da ba su da tabbas a kansu, wadanda za su iya gurgunta zaman lafiya da hadin kan ‘yan kasa”, in ji Ebienfa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp