Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta ce tana da kwararan hujjoji da ke tabbatar da zargin neman yin lalata (zina) da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bukata a wurinta.
Natasha, wacce ta yi magana ta bakin lauyanta, Victor Giwa, ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga kalaman da matar Akpabio, Unoma ta yi.
Matar Akpabio a ranar Juma’ar da ta gabata don kare martabar mijinta, ta yi barazanar maka Sanata Natasha a gaban kotu kan zargin da ta yi wa mijinta.
Sai dai, a martanin da ta yi ta bakin lauyanta a ranar Asabar, Giwa ya bukace matar Sanata Akpabio ta da janye kanta a rikicin don bai wa mijinta damar kare kansa saboda wanda yake karewa tana da “kwakkwarar hujja da za ta tabbatar da zarginta.”
Sanata Natasha ta kai karar Akpabio da mai taimaka masa, Mfon Patrick gaban kotu, inda ta bukaci diyyar Naira Biliyan 100.3 bisa zargin bata mata suna bayan takaddamar da ta biyo bayan sauya mata kujera a zauren majalisar dattawa.
Sanata mai wakiltar Kogi ta Arewa, wacce aka dakatar kuma aka mika wa kwamitin da’a na majalisar dattawa koke akanta, a yayin wata hira da gidan talabijin, ta ce, Sanata Akpabio ya ki amincewa da bukatarta kan yanayin kamfanin karafa na Ajaokuta saboda ta ki amincewa da buƙatar shi na neman yin lalata da ita.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp