• English
  • Business News
Wednesday, August 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zargin Sin Da Hannu A Ta’addanci A Nijeriya: Tuggu, Makirci Ne Da Kisisinar Turawan Yamma

by Abdulrazaq Yahuza
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Zargin Sin Da Hannu A Ta’addanci A Nijeriya: Tuggu, Makirci Ne Da Kisisinar Turawan Yamma
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A tsakiyar watan Afrilu ne wata jaridar da ake wallafawa a Birtaniya (The Times) ta yi wani rahoto da ya yi zargin ‘wai’ wasu Sinawa da ke aiki a Nijeriya musamman bangaren ma’adanai suna daukar nauyin ta’addanci a wasu sassa na Nijeriya domin kawai su fake da guzuma su harbi karsana.

Tun daga lokacin da jaridar ta fitar da rahoton ana ci gaba da samun martanoni daban-daban daga masharhanta masu adalci wadanda suke rabe tsaki da tsakuwa. Shi ma ofishin jakadancin Sin da ke Nijeriya ya fitar da sanarwar manema labarai a kan karyata zargin mara tushe balle makama.

  • Ter Stegen Ya Kafa Sabon Tarihi A Barcelona

Idan aka bi rahoton jaridar kan lamarin, za a tarar zargin nata ya ta’allaka ne a kan wata shadara guda daya tak, da ke cewa “shugabannin ‘yan ta’adda sun bugi kirjin cewa a yanzu wuyansu ya isa yanka, hatta Sinawan da ke son aiki (hakar ma’adanai) a yankunan da suke dole su biya kudin haya.” Kuma fa wannan din ma an tsinto ne a wani bidiyo da ke gararamba a shafukan sada zumunta.

Idan aka ce an ga wani abu a shafukan sada zumunta, (galibi mu a Nijeriya) ba a daukar abin da muhimmanci har sai an tabbatar da shi daga daya daga cikin shafukan sahihan gidajen jaridu ko takwarorinsu na kafafen yada labarai na lantarki. Domin akwai masu shirya bidiyo ko kirkiro da labari da nufin janyo hankulan jama’a a shafinsu (traffic) saboda taro da sisi da za su iya samu da hakan. A kan wannan, na san da yawa sun yi watsi da rahoton a matsayin zuki ta malle.

Kazalika, ni ban yi mamaki ba da na ji cewa wata jaridar Birtaniya ce ta wallafa rahoton, domin duk mai bibiyar yadda kawancen Sin da Afirka ke bunkasa ci gaba a kasashenmu, ya san da zaman Turawan Yamma ba za su kyale ba, dole za su rika hada tuggu da kisisina da makirce-makircen wargaza lamarin. Domin su sun kasa yin hakan saboda mugunta. Mu dauki misali daga mulkin mallakar da suka yi wa Afirka, tatsar yankin suka yi maimakon kawo masa ci gaba, da yawan masana tarihi sun bayyana cewa da arzikin Afirka ne aka gina Turai. Ta hanyar bautarwa ko cinikin bayi da sace-sacen ma’adanai da suka yi zuwa kasashensu.

Labarai Masu Nasaba

Kasar Sin Ta Sanar Da Matakan Fara Bayar Da Ilimin Kafin Firamare Kyauta

Shugaban IWGA: Birnin Chengdu Zai Karbi Bakuncin Gasar Wasanni Mafi Kyau A Tarihi

To ma wai, me ya sa Turawan Yamma ba za su yi irin wannan bakin kishin ba, Sin ta samu karbuwa dari bisa dari a Afirka, saboda ta bude wa nahiyar kofofin bunkasa tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa. Sin ta gina layukan dogo sama da kilomita 6,000, titunan mota sama da kilomita 6,000, kusan tasoshin teku 20 da kuma manyan tashoshin wutar lantarki sama da 80 a Afirka. Bugu da kari, ta taimaka wajen gina asibitoci da dakunan shan magani sama da 130, da makarantu sama da 170, da filayen wasanni 45 da kuma aiwatar da ayyukan bunkasa noma sama da 500 duk a Afirka.

Yadda mutum zai fahimci alherin da ke cikin wadannan ayyukan shi ne, a Nijeriya, Sin ta gina katafariyar tashar tekun da babu kamarta kaf a Yammacin Afirka a Lekki da ke Jihar Legas. Ana sa rai wannan tashar, ta samar da kudi kusan Dala Biliyan 360 tare da samar da aikin yi akalla Dubu Dari da Saba’in (170,000).

Ke nan me ya sa Turawan Yamma ba za su yi hassada ba, tun da sun riga Sin zuwa nahiyar da shekaru aru-aru amma ba su tsinana komai ba sai bautarwa da sace-sacen dukiyar yankin? Hatta lokacin da suka ce sun bai wa kasashen Afirka ‘yancin cin gashin kai, ba su amince kasashen sun karbi ragamar tafiyar da tattalin arzikinsu ba sai bayan wasu shekaru da suka ga uwar-bari.

Misali mu a Nijeriya, an ba mu ‘yancin kai daga Ingila a 1960, amma ragamar tafiyar da tattalin arzikin kasa bai dawo hannun shugabanninmu baki daya ba sai a 1963.
Abin da Turawan Yamma suka fi kwarewa a kai shi ne kulle-kulle da makirce-makirce a kasashen duniya. Sun fi so su ga ana gwabza yaki a tsakanin ‘yan kasa don wargaza kasa. Misalin abin da ya faru a Libiya ya isa zama shaida, sannan kwanan nan ga gobarar da suka kunna a Sudan.

Ita kuwa Sin, salonta ya bambanta, tana mutunta ‘yancin kasashen da take kawance da su, ta fi yarda da cin gajiyar juna maimakon kashin dankali, ta fi son yaukaka zumunci da inganta zaman lafiya maimakon tashin-tashina. Kokarin da Sin ta yi na sake hade kan Saudiyya da Iran a ‘yan kwanakin baya manuniya ce kan haka.

Tabbas! Lokaci ya yi da Afirka za ta kara nuna wa Turawan Yamma cewa kan mage ya waye, muna bukatar abokan ci gaba ne ba masu kawo koma-baya ba, masu mutunta ‘yancinmu ba masu tilasta mana auren jinsi da keta mana kyawawan al’adu da muka gada ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Amurka Mai Matukar Son Amfani Da Karfin Tuwo Ta Zama Sanadin Tashin Hankalin Duniya

Next Post

Mene Ne Hukuncin Hada Sittu Shawwal Da Ramuwar Ramadan?

Related

Kasar Sin Ta Sanar Da Matakan Fara Bayar Da Ilimin Kafin Firamare Kyauta
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Sanar Da Matakan Fara Bayar Da Ilimin Kafin Firamare Kyauta

4 hours ago
Shugaban IWGA: Birnin Chengdu Zai Karbi Bakuncin Gasar Wasanni Mafi Kyau A Tarihi
Daga Birnin Sin

Shugaban IWGA: Birnin Chengdu Zai Karbi Bakuncin Gasar Wasanni Mafi Kyau A Tarihi

4 hours ago
Matakin Baiwa Kansa Hakuri Ba Zai Kawar Da Matsayin Gwamnatin Lai Ching-te Na Kasancewa ’Yar Dara A Hannun Amurka Ba
Daga Birnin Sin

Matakin Baiwa Kansa Hakuri Ba Zai Kawar Da Matsayin Gwamnatin Lai Ching-te Na Kasancewa ’Yar Dara A Hannun Amurka Ba

5 hours ago
Sin Ta Fitar Da Shirin Kyautata Muhalli Domin Inganta Kiwon Lafiya Na Shekaru Biyar
Daga Birnin Sin

Sin Ta Fitar Da Shirin Kyautata Muhalli Domin Inganta Kiwon Lafiya Na Shekaru Biyar

5 hours ago
Sashen Cinikayyar Samar Da Hidimomi Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso Takwas A Rabin Farko Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Sashen Cinikayyar Samar Da Hidimomi Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso Takwas A Rabin Farko Na Shekarar 2025

7 hours ago
Gwamnatin Sin: Gwamnatin Jama’a Domin Jama’a
Daga Birnin Sin

Gwamnatin Sin: Gwamnatin Jama’a Domin Jama’a

7 hours ago
Next Post
Mene Ne Hukuncin Hada Sittu Shawwal Da Ramuwar Ramadan?

Mene Ne Hukuncin Hada Sittu Shawwal Da Ramuwar Ramadan?

LABARAI MASU NASABA

Kwamishinan Sufuri Ya Yi Murabus Kan Belin Wani Da Ake Zargi Da Laifin Safarar Kwaya A Kano

Kwamishinan Sufuri Ya Yi Murabus Kan Belin Wani Da Ake Zargi Da Laifin Safarar Kwaya A Kano

August 6, 2025
Hare-haren Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Ya Ragu A Cikin Shekaru Biyu – Ribadu

Hare-haren Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Ya Ragu A Cikin Shekaru Biyu – Ribadu

August 5, 2025
Kasar Sin Ta Sanar Da Matakan Fara Bayar Da Ilimin Kafin Firamare Kyauta

Kasar Sin Ta Sanar Da Matakan Fara Bayar Da Ilimin Kafin Firamare Kyauta

August 5, 2025
Shugaban IWGA: Birnin Chengdu Zai Karbi Bakuncin Gasar Wasanni Mafi Kyau A Tarihi

Shugaban IWGA: Birnin Chengdu Zai Karbi Bakuncin Gasar Wasanni Mafi Kyau A Tarihi

August 5, 2025
Jigawa Ta Fitar Da ₦1.5bn Na Lamunin Noma Ga Ma’aikatan Gwamnati Kashi Na Biyu

Jigawa Ta Fitar Da ₦1.5bn Na Lamunin Noma Ga Ma’aikatan Gwamnati Kashi Na Biyu

August 5, 2025
Matakin Baiwa Kansa Hakuri Ba Zai Kawar Da Matsayin Gwamnatin Lai Ching-te Na Kasancewa ’Yar Dara A Hannun Amurka Ba

Matakin Baiwa Kansa Hakuri Ba Zai Kawar Da Matsayin Gwamnatin Lai Ching-te Na Kasancewa ’Yar Dara A Hannun Amurka Ba

August 5, 2025
Sin Ta Fitar Da Shirin Kyautata Muhalli Domin Inganta Kiwon Lafiya Na Shekaru Biyar

Sin Ta Fitar Da Shirin Kyautata Muhalli Domin Inganta Kiwon Lafiya Na Shekaru Biyar

August 5, 2025
Ruftawar Gini Ya Kashe Uwa Da ‘Ya’yanta Biyar A Katsina

Ruftawar Gini Ya Kashe Uwa Da ‘Ya’yanta Biyar A Katsina

August 5, 2025
Sashen Cinikayyar Samar Da Hidimomi Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso Takwas A Rabin Farko Na Shekarar 2025

Sashen Cinikayyar Samar Da Hidimomi Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso Takwas A Rabin Farko Na Shekarar 2025

August 5, 2025
Gwamnatin Sin: Gwamnatin Jama’a Domin Jama’a

Gwamnatin Sin: Gwamnatin Jama’a Domin Jama’a

August 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.