Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kara tabbatar da amincewarsa ga shugaban ma’aikatansa (CoS), Femi Gbajabiamila.
Sake nanata amincewar shugaban kasar ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar, na zuwa ne biyo bayan zarge-zargen da ake yi masa na nadin mukamai ta hanyar nuna wariya.
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa Kan Raya Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Tsakanin Sin Da Girka
- Akwai ‘Yancin Tofa Albarkacin Baki A Gwamnatin Tinubu – Minista
Tinubu wanda ya yi magana gabanin fara taron majalisar zartarwa ta tarayya a fadar shugaban kasa a jiya Litinin, ya kafa wasu ka’idojin gudanar da taron.
Da yake jawabi ga matsalolin da ya lura da su, ciki har da shiga zauren majalisar ba tare da izini ba, Shugaba Tinubu ya jaddada bukatar magance matsalolin cikin gaggawa.
Ya ce, kamar kowa, yana iya yin kuskure kuma idan hakan ta faru, a lura kuma a yi gaggawar gyara su.
Shugaban ya bayyana cikakken kwarin guiwarsa ga amincin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin, inda ya yi kira da a kawo karshen duk wani yunkurin batanci ga shugaban.