Wani tela mai suna Kenneth ya bugawa tsohuwar masoyiyarsa wuka, Ebenezer Agada wanda ya yi sanadin mutuwarta har lahira bisa zarginta da yaudararshi.
Bincike ya nuna cewa Kenneth ya taso daga Makurdi ne zuwa Kaduna, ya sauka a daya daga cikin otal din da ke kan titin Waff road kusa da inda tsohuwar masoyiyarsa Ebenezer ke aiki.
An samu cewa, Kenneth ya ta kiran Ebenezer a wayar tarho amma taki amsa kiransa, sabida hakan ya fara shirin yadda zai dau fansa kan kin amsa kiransa.
Sai dai Kenneth, wanda kotun majistare ta Kaduna ta tura shi gidan kaso a ranar 20 ga Afrilu, 2023 ya bayyana cewa yayin da ya gaza shawo kan Ebenezer, kawai sai ya yanke shawarar zuwa Kasuwar Central market ya siyo Wuka ta Naira N2,000 sannan ya wasa ta bayan ya dawo masauki, sannan ya jira zuwa wani lokaci da ya shirya aikata ta’asarsa.
Wanda ake zargin ya ce shi sana’ar dinkin kaya yake yi, kuma ya kashe makudan kudi akan Marigayiyar, wanda ya ce sun shafe shekaru 6 suna tare.