Dan wasan kwallon tebur ta Snooker daga kasar Sin Zhao Xintong ya zamo dan nahiyar Asiya na farko da ya lashe gasar Snooker ta kasa da kasa, bayan ya yi nasara kan abokin fafatawarsa Mark Williams dan yankin Wales da maki 18 da 12, a wasan karshe da suka buga jiya Litinin.
Yanzu haka dai Zhao zai fara buga wasannin kakar dake tafe a matsayin dan wasa na 11 a duniya, kuma akwai ’yan wasa Sinawa 9 da su ma ke cikin matsayi na 32 a saman jadawalin kwararrun ’yan wasan na duniya.
- Zulum Ya Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira 6,000 Garuruwansu A Borno
- Saudiyya Ta Tanadi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Yin Aikin Hajji Babu Takardun Izini
Kafin wannan lokaci, Ding Junhui ne dan wasan Asiya na farko da ya taba kaiwa ga wasan karshe na gasar Snooker ta kasa da kasa a shekarar 2016, ko da yake ya gamu da rashin nasara a hannun abokin karawarsa Mark Selby.
Da yake tsokaci game da wasan na karshe na jiya, Mark Williams daga yankin Wales, ya ce Zhao abokin karawa ne mai hazaka. Don haka ba abun da zai fada game da shi illa jinjinawa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp