ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zulum Ya Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira 6,000 Garuruwansu A Borno

by Sadiq
1 year ago
Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya mayar da iyalai 6,000 da suka rasa matsuguninsu saboda hare-haren Boko Haram zuwa garuruwansu na asali.

Yawancin mutanen sun fito ne daga ƙananan hukumomin Dikwa da Mafa.

  • Aikin Hajjin 2025 Ya Fara A Hukumance Yayin Da Tawagar NAHCON Ta Musamman Ta Tashi Zuwa Makkah
  • Jiragen Kasa Na Sin Sun Yi Jigilar Fasinjoji Sama Da Miliyan 100 A Lokacin Hutun Ranar Ma’Aikata

Gwamna Zulum ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna da ke Maiduguri, inda aƙalla iyalai 11,000 ke zaune saboda rikicin da ya daɗe yana faruwa a jihar.

ADVERTISEMENT

Ya ce dole ne a mayar da mutane gidajensu saboda yawaitar aikata laifuka a cikin sansanin, ciki har da karuwanci, tada zaune tsaye, cin zarafin yara da sauran muggan laifuka.

“Boko Haram ba za ta ƙare ba sai an dawo da jama’a gida su fara rayuwa yadda ya kamata,” in ji Zulum.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

“Mun rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke cikin Maiduguri. Yanzu haka saura biyu da ba na hukuma ba. Mun riga mun dawo da kashi 75 na ‘yan sansanin Muna gida, saura kashi 25 za su koma cikin kwanaki masu zuwa.”

Kowane iyali sun samu tallafin abinci, kayan gini da kulawar lafiya.

Haka kuma, kowane magidanci mace ko namiji za a ba shi Naira 100,000, yayin da matan gidan za su ƙara samun Naira 50,000 don taimaka musu da buƙatunsu na yau da kullum.

Za a Ƙara Inganta Cibiyar Koyo Sana’o’i a Gidan Gyaran Hali

Tun da safiyar ranar Litinin, Gwamna Zulum ya kai ziyara gidan gyaran hali na manyan laifuka da ke Maiduguri.

Ya ce za a inganta cibiyar koyar da sana’o’i da ke gidan don taimaka wa fursunoni su koyi sana’a da za su yi amfani da ita bayan an sake su.

“Manufar ɗaure mutum a gidan gyaran hali ita ce gyara halayensa, ba wai tsare shi kawai ba. Wannan ba zai yiwu ba sai akwai kayan aikin koyarwa da ake buƙata” in ji Zulum.

“Za mu duba wasu daga cikin fursunonin da ke da ƙananan laifuka, mu gani ko akwai yiwuwar a sake su bisa doka.”

Zulum ya samu rakiyar ɗan Majalisar Tarayya, Bukar Talba, shugaban ma’aikatansa na riƙon ƙwarya, mai ba shi kan harkokin addini da wasu jami’an gwamnati.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 6 A Ƙauyukan Filato, Sun Jikkata Wasu

‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 6 A Ƙauyukan Filato, Sun Jikkata Wasu

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.