• English
  • Business News
Sunday, June 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zhao Yingxin: Mace Ta Farko Da Ta Rike Matsayin Shugabar Masu Daukar Hoto A Tarihin Wasannin Olympics Na Duniya

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Kasar Sin
0
Wasannin Olympics

•Madam Zhao Yingxin tare da abokan aikinta na kasashen waje, bayan bikin bude wasannin Olympics na Beijing na shekarar 2008

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Zhao Yingxin, ita ce mataimakiyar shugabar kungiyar mata masu daukar hoto ta kasar Sin kuma shugabar jaridar yada labarai ta hotuna ta kasar Sin. Yayin wasannin Olympics na Beijing a 2008, Zhao ta zama mace ta farko da ta rike matsayin shugabar masu daukar hoto a tarihin wasannin Olympics na duniya. Haka kuma, ita ce ’yar kasar Sin ta farko da ta rike wannan matsayi. A 2022, Zhao ta adana gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta Beijing ta hanyar kyamararta, kuma ta shaida gasannin wasannin Olympics guda biyu da Beijing ta karbi bakuncinsu ta hanyar kyamararta.

Tsohon shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC, Juan Antonio Samaranch, ya taba cewa, “kafafen yada labarai su ne alkalan karshe na wasannin Olympics. Dole ne mu yi kokarin gamsar da dukkan ’yan jarida.” ’Yan jarida masu daukar hoto muhimman mahalarta ne kuma masu yada labaran wasannin. Hotunan da suke dauka masu ban sha’awa bisa kwarewa, na yaduwa da kuma jan hankalin duniya. Shugaban masu daukar hoto, matsayi ne mai muhimmanci, saboda mai rike da mukamin ne ke jagorantar kowanne mai daukar hoto dake da rejista, yayin wasannin.

  • Bikin Baje-Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Afirka Zai Kara Inganta Hadin-Gwiwar Bangarorin Biyu

Bisa kundin jagorancin na kwamitin IOC, lallai ne kwamitin ya sanar da sunan shugaban masu daukar hoto, shekaru 3 kafin lokacin wasannin. Kuma dole shugaban ya kasance kwararre a fannin daukar hotunan wasannin kasa da kasa, kuma ya fahimci yadda ayyukan yada labaran wasannin ke gudana, sannan ya kasance mai kwarewa a fannin mu’amala da harkokin shugabanci, kana ya iya Turanci sosai.

A watan Afrilun 2005, shekaru 3 kafin wasannin Olympics na Beijing na 2008, lokacin da kwamitin shirye-shiryen wasannin Olympics na 2008 na Beijing ya yanke shawarar daukar shugaban masu daukar hoto, kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya gabatar da sunan Zhao Yingxin, a lokacin ita ce kwararriyar mai daukar hotunan wasanni ga Xinhua. A don haka, ta zama mace ta farko da ta rike matsayin a tarihin wasannin Olympics.

Zhao ce ke da alhakin kula da harkokin sadarwa da na gudanarwa da na tafiyar da ayyukan da suka shafi daukar hotunan wasannin, ciki har da shirya yadda aikin daukar hotunan wasannin 28 a wuraren wasa 37 za su kasance da kuma kebe wani wuri na musammam ga masu daukar hoto.

Labarai Masu Nasaba

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

Haka kuma, ita ce ke da alhakin dauka da horar da mambobi 80 na tawagar jagororin masu daukar hoto da mataimakansu, da wani ayarin ’yan sa kai sama da 200. Wadannan mutane sun samu horo kafin a ba su aiki a wuraren wasannin daban-daban.

Wasannin Olympics
•Madam Zhao Yingxin yayin da take bakin aiki a wasannin Olympics na Athens a shekarar 2004

“Aiki ne mai matukar wahala, dole sai mutum ya shirya sosai,” cewar Anthony Edgar, shugaban sashen yada labarai na kwamitin IOC a wancan lokaci, yayin da ya hadu da Zhao a karo na farko.

Domin tabbatar da gudanar da aikin cikin nasara, Zhao da tawagarta, sun yi iyakar kokarinsu wajen hidimtawa masu daukar hoto yadda ya kamata, kuma sun samu yabo sosai daga masu daukar hoton. A littafinta mai suna, First Woman Photo Chief in Olympic History, wato mace ta farko da ta rike mukamin shugabar masu daukar hoto a tarihin wasannin Olympics, Zhao ta zayyana dalla-dalla, aiki tukuru da ta yi yayin wasannin Olympics na Beijing.
Zhao da tawagarta sun shiga cikin aikin shirya bikin bude wasannin, watanni 6 kafin lokacin gudanar da shi, sun kuma kara fahimtar dukkan batutuwa da abubuwan da suka shafi bikin budewar.

Sun kebe wasu wurare 13 ga masu daukar hoto a wuraren masu sharhin wasannin a filin wasa na “Shekar Tsuntsu”, wato Bird’s Nest a Turance. Haka kuma, sun tanadi kujeru 300 ga masu daukar hoto a cikin ’yan kallo, sun kuma kebe wani wuri ga masu daukar hoto a wajen filin wasannin, domin su dauki hotuna daga nesa da za su kunshi kowacce kusurwa, a yayin bikin budewar da na wasannin tartsatsin wuta.

Akwai sadarwar intanet na VLAN a dukkan wuraren da aka kafa domin editoci da masu daukar hoto. An ba masu daukar hoto damar amfani da sadarwar ta VLAN wajen tura hotunnan da suka dauka kai tsaye ga editocinsu. Wannan shi ne karon farko da aka yi amfani da VLAN yayin wasannin Olympics domin aikewa da hotuna kai tsaye a lokacin da aka dauka.

Wasannin Olympics
•Madam Zhao a filin wasan zamiyar kankara kafin bude wasannin Olympics na lokacin hunturu na na 2022 a Beijin

Yayin wasannin Olympics na lokacin hunturu na 2022, da aka gudanar tsakanin ranar 2 zuwa 20 ga watan Fabrairu, a matsayinta na mambar tawagar masu daukar hotunan Olympics na kungiyar masu daukar hotuna ta kasar Sin, a karon farko, Zhao ta wakilci Jaridar yada labarai ta hotuna ta kasar Sin, wajen daukar hotunan wasannin Olympics.

Zhao ta ce, “akwai masu daukar hotunan yada labarai 735 da aka yi wa rejista domin wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, daga cikinsu kuma, 140 Sinawa ne. Kuma ina alfaharin kasancewa daya daga cikinsu.”
A daren ranar 14 ga watan Fabrairun, yanayin sanyi ya kai maki 20 kasa da sifiri, a yankin dusar kankara na Genting, a birnin Zhangjiakou dake lardin Hebei na arewacin kasar Sin. Xu Mengtao mai shekaru 31 ta fafata a gasar wasan kankara ta Aerial Freestyle.

Tsallen Xu na karshe ya yi kyau sosai. Kuma ita ta lashe lambar zinare ta farko ga kasar Sin a irin wannan gasa ta Aerial Freestyle. “A karshe na yi nasara! Na yi nasara!” cewar Xu cikin daga murya. Zhao Yingxin ta dauki hoton wannan lokaci na murna. Ta tsaya da kyamararta cikin dusar kankara sama da tsawon sa’o’i 4 yayin gasar. Zhao ta je yankin na Genting yayin wasannin har sau 5 domin daukar hotunan ‘yan wasa.

Wasannin Olympics
adam Zhao Yingxin (tsakiya) yayin da take tattaunawa da manema labarai, a matsayinta na shugabar masu daukan hoto a lokacin wasannin Olympics na 2008 a Beijing

Beijing ya zama birni na farko da ya karbi bakuncin wasannin Olympics na lokacin zafi da na hunturu a tarihi. Yayin bikin rufe wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, idanun Zhao sun cika da hawaye a lokacin da ta ji taken wasan Olympics na Beijing na 2008, mai suna You and Me, wato Ni da kai, yayin da zobban tambarin Olympics suka daga sama. Wannan ya tuna mata da shekarar 2008.

Yayin hirarraki sama da 30 a lokacin wasannin, Zhao ta dauki dimbin hotunan ’yan wasan kasar Sin da suka lashe lambobin yabo dake kokarin cimma burikansu a wasannin Olympics, inda ta dauki hotunan da suka nuna kauna da goyon bayan dake tsakanin ’yan wasa daga dukkan kasashe yayin da ake fuskantar annoba a duniya. Ta kuma dauki hotunan ma’aikatan sa kai da masu aikin kandagarki da takaita yaduwar annoba dake nuna yadda suke cike da kauna da kulawa. Hotunanta sun dauki yanayi mai aminci da kayatarwa na wasannin Olympics, haka kuma suna kunshe da ruhin wasannin Olympics na Beijing.

Zhao Yingxin ta fara sha’awar wasan kwallon tebur a lokacin da take makarantar firamare, daga nan ne kuma ta fara kaunar wasannin motsa jiki.

Ta karanci bangaren daukar hotunan yada labarai a lokacin da ta yi dalibta a sashen nazarin aikin jarida na jami’ar Renmin a Beijing. Bayan ta kammla, ta zama mai daukar hoto dake aiki da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. A shekarar 1993, ta fara aiki a kasar Birtaniya a matsayin mace mai daukar hoto ta farko da Xinhua ya tura ketare.

Yayin da take aiki da Xinhua, ta dauki hotunan muhimman lokuta da dama, kamar na dawowar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, da cikar jamhuriyar jama’ar kasar Sin shekaru 50 da kafuwa, da damar da Beijing ya samu na karbar bakuncin wasannin Olympics, da wasannin Olympics na lokacin hunturu na birnin Salt Lakes a 2002, da wasannin Olympics na Athens a shekarar 2004. Ta kan dauki kayayyakin daukar hoto kamar takwarorinta maza, kuma tana daukar hotuna masu kyau da inganci kamarsu. Zhao ta ce, “zan iya aiki da kyau kamar yadda maza za su yi ko ma fiye da su. Ta hakan ne kawai za a samu sabbin masu daukar hoto na ban mamaki.”
A ganinta, mata masu daukar hoto sun fi mayar da hankali fiye da maza. A ko da yaushe, Zhao na son daukar hoton idanun ’yan wasa yayin da ake fafatawa a gasa, saboda idanunsu za su fi taba zuciyar ’yan kallo. “Daukar hotuna yayin da ake tsaka da fafatawa a gasa, shi ne zai bayyana irin karfin zuciyar ’yan wasa”, cewar Zhao.

Wasannin Olympics
•Hoton wani dan wasa da madam Zhao ta dauka a wasannin Olympics na 2008 a Beijing

A ganin wasu mutane, a wasu lokuta a kan yi rashin nasarar daukar hoto yayin wasannin Olympics, saboda lokaci ne da ba zai maimaitu ba. Amma wannan shi ne sirrin zama mai daukar hoton wasannin, saboda ana yin wasannin ne kai tsaye, don haka dole ne mai daukar hoto ya mayar da hankali matuka domin daukar hotunan lokuta mafiya kayatarwa. A sana’arta, Zhao ta ga kayatattun lokuta, da masu taba zuciya da ma wadanda suka shiga tarihi.

Chen Lu ta kasance zakarar wasan zamiyar kankara na Figure Skating na farko a kasar Sin. Zhao ce kadai Basiniya mai daukar hoto a wajen, a lokacin da Chen ta lashe lambar zinare a gasar zakarun duniya na zamiyar kankara a 1995 a Birmingham na Birtaniya. Zhao ta dauki hoton idanun Chen a lokacin da take farin cikin lashe lambar yabon.

Shekaru 7 bayan nan, Zhao ta halarci wasannin Olympics na lokacin hunturu na birnin Salt Lake a shekarar 2002, kuma ta shaida wani muhimmin tarihi a lokacin da Yang Yang ta lashe lambar zinare na farko a wasannin Olympics na tseren kan kankara na gajeren zango mai mita 500. Zhao ta tuna da idanun Yang Yang a lokacin da take fafatawa a matakin karshe na gasar. Abun da Zhao ta gani a idanun Yang, wani irin kuzari ne na kokarin cimma burinta na wasannin Olympics, da kuma ainihin ruhin wasannin na Olympics.

Zhao ta ce, “a shekarun da na daukar hotuna, ba shaida raunikan da ’yan wasa suka ji kadai na yi ba, har ma da irin kuzari da karsashin da suke da shi ga wasanni. Bayan daukar hotunan wasannin Olympics, na kara fahimtar ruhin wasannin.”

Zhao wadda a baya daliba ce, da ke kaunar wasan kwallon tebur kuma mai daukar hotunan wasanni, kana shugabar masu daukar hotunan wasannin Olympics, ta kasance mai samun kwarin gwiwa daga ruhin wasanni. Ba ta taba yin kasa a gwiwa a kokarinta na samun ci gaba ba. Littafinta na “First Woman Photo Chief in Olympic History”, ya bayyana aikin da ta yi a matsayin shugabar masu daukar hotunan wasannin Olympics da kuma aikinta a matsayin mai daukar hoto. Ta hanyar labaran da ta bayar, littafin ya zayyana gwagwarmayar wani zamani.

Lokaci na sauyawa, kuma Zhao ma na sauyawa. Amma kaunarta ga wasanni, da daukar hoto da ma jajircewarta wajen cimma burin aikinta, ba za su taba sauyawa ba. Ta yi ammana cewa, daukar hoto da yadda hoton ke jan hankali da ma aikewa da sako, zai taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihi da ma inganta ci gaban al’umma.
A zamanin da hotuna suka yi fice, fasaha za ta iya sauya yadda ake daukar hotuna da adana su, kuma za ta iya saukaka aikin daukar hoto, amma kuma ba za a taba maye gurbin zuciya da basirar kwararren mai daukar hoto ba.

Zhao na fatan karin masu daukar hoto za su taimaka wajen amfani da kyamarorinsu domin adana tarihin wannan muhimmin zamani, kuma za su taimakwa wajen samar da ingantattun hotuna.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Mahalarta Taron Davos Sun Ba Da Labarin Ci Gaban Sin

Next Post

Za Mu Nome Dazuka Don Magance Matsalar Tsaro A Neja – Bago

Related

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

4 months ago
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

12 months ago
wang lili
Daga Kasar Sin

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

12 months ago
Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura
Daga Kasar Sin

Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura

1 year ago
Zambiya
Daga Kasar Sin

’Yar Kasar Zambiya: A Nan Kasar Sin, Ina Jin Tamkar Ina Gida!

1 year ago
Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Daga Kasar Sin

Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

1 year ago
Next Post
Za Mu Nome Dazuka Don Magance Matsalar Tsaro A Neja – Bago

Za Mu Nome Dazuka Don Magance Matsalar Tsaro A Neja - Bago

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Adawa Da Duk Wata Yarjejeniyar Haraji Da Ka Iya Illata Moriyarta

Sin Na Adawa Da Duk Wata Yarjejeniyar Haraji Da Ka Iya Illata Moriyarta

June 29, 2025
2027: Ƴan Adawa Na Ƙara Ƙaimin Kawar Da Tinubu

2027: Ƴan Adawa Na Ƙara Ƙaimin Kawar Da Tinubu

June 29, 2025
Yadda Yaƙin Iran Da Isra’ila Zai Iya Shafar Zamantakewa Da Tattalin Arziƙin Nijeriya

Yadda Yaƙin Iran Da Isra’ila Zai Iya Shafar Zamantakewa Da Tattalin Arziƙin Nijeriya

June 29, 2025
Ƙwallon Mata: Rivers United Ta Doke Nasarawa Amazons A Wasan Ƙarshe Na Kofin Shugaban Ƙasa

Ƙwallon Mata: Rivers United Ta Doke Nasarawa Amazons A Wasan Ƙarshe Na Kofin Shugaban Ƙasa

June 29, 2025
Xi Ya Yi Kira Ga Mazauna Wani Kauye Dake Xizang Da Su Rike ‘Yan Uwantakar Kabila

Xi Ya Yi Kira Ga Mazauna Wani Kauye Dake Xizang Da Su Rike ‘Yan Uwantakar Kabila

June 29, 2025
Zaben 2027 Yaƙi Ne Tsakanin Talakawa Da Masu Mulki – Sanata Kaita 

Zaben 2027 Yaƙi Ne Tsakanin Talakawa Da Masu Mulki – Sanata Kaita 

June 29, 2025
Gyaran Tsarin Mulki: Majalisa Ta Shirya Sauraron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Wasu Sassan Nijeriya

Gyaran Tsarin Mulki: Majalisa Ta Shirya Sauraron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Wasu Sassan Nijeriya

June 29, 2025
Yara 150,000 Ake Haifa Da Cutar Sikila A Nijeriya Duk Shekara – Rahoto

Yara 150,000 Ake Haifa Da Cutar Sikila A Nijeriya Duk Shekara – Rahoto

June 29, 2025
Mutuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Gov Ododo

Mutuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Gov Ododo

June 29, 2025
Jirgin Alhazai Na Farko Ya Iso Jihar Jigawa

Jirgin Alhazai Na Farko Ya Iso Jihar Jigawa

June 29, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.