Ministan kula da harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a na kasar Zimbabwe Jenfan Muswere, ya jinjinawa jarin kasar Sin, yana cewa ya bunkasa karfin samar da siminti a kasar.
Da yake jawabi ga manema labarai jiya Talata a Harare babban birnin kasar, ministan ya ce kamfanonin kasar Sin sun zuba jarin sama da biliyan 1 cikin shekara daya da ta gabata a masana’antun samar da siminti na Zimbabwe.
Ya ce karuwar jarin na Sinawa ta dace da kokarin gwamnatin kasar na farfado da bangaren samar da kayayyaki da gaggauta bunkasa ayyukan masana’antu na kasar.
A cewar ministan, shirin sake gina bangaren samar da kayayyaki da samar da ci gaba wanda na wucin gadi ne tsakanin manufar bunkasa ayyukan masana’antu ta kasar da wa’adinta ya kare da kuma sabuwar manufa ta shimfida tubali mai kwari ga ajandar bunkasa masana’antu ta kasar.
Ya kara da cewa, bangaren samar da kayayyaki wanda ya mamaye kaso 15.3 na alkaluman GDP na Zimbabwe a 2024, shi ne kan gaba wajen ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar. (Mai fassara: Fa’iza)