Abokai, yanzu haka sabon ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, yana ziyarar aiki a wasu kasashen Afrika. Ziyarar da duk ministan harkokin wajen Sin yake kaiwa Afrika a sabuwar shekara cikin jerin shekaru 33.
Tun kafuwar sabuwar jamhuriyyar jama’ar kasar Sin, kasar ta sha fama da talauci da koma baya, kuma ita da kasashen Afrika sun taimakawa juna, da goyawa juna baya, da ma amincewa da manyan muradunsu, don samun bunkasuwa tare cikin hadin kai. Har zuwa yanzu, Sin tana samun bunkasuwar a zo a gani a duniya, har ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya, ba ta manta da abokanta na Afrika ba ko kadan, tana kuma kokarin more fasahohi, da samar da tallafi don cimma moriya tare.
Sin ba ta canja matsayinta kan huldarta da kasashen Afrika ba tun kafuwar huldarsu, kuma ziyarar FMn kasar a ko wace shekara ta tabbatar da dangantakarsu, kuma ci gaban da suke samu a bangarori daban-daban a cikin dogon lokaci ya shaida zumuncinsu. (Mai zane da rubuta: MINA)