Ci gaba daga makon jiya…
Imamul Fakihani, ya ce “wurin da aka binne Manzon Allah (SAW) ya fi sama ya fi kasa”. Haka nan, Alkadiy Iyad ya ce “Babu wani wurin da ya kai a hada shi da wurin da aka binne jikin Manzon Allah (SAW) saboda abu biyu: na farko, cewar da aka yi ko wane mutum ana binne shi a kasar da aka yi shi da ita, to nan wurin da aka binne Manzon Allah (SAW) kasar jikinsa ne, to wane abu ne za a iya hada shi da jikinsa (SAW)? Na biyu, bisa irin Mala’ikun da suke sauka a nan wurin, da irin albarkar da take sauka, da salatin da ake aikawa da sauran alheran da ke sauka a wurin, babu wani wurin da ya kai shi.”
Abu Ya’ala ya ruwaito Hadisi daga Sayyidina Abubakar (RA) ya ce, ya ji Manzon Allah (SAW) ya ce “Allah ba ya karbar Annabinsa sai a wurin da Annabin ya fi so.” Sayyidina Abubakar ya fadi Hadisin ne lokacin da Annabi (SAW) ya yi wafati sa’ilin da aka samu sabani kan wuri mafi dacewa a binne shi (SAW). Saboda haka suka ce babu shakka wurin da Annabi (SAW) ya fi so, nan ne Allah ya fi so. Domin son sa, yana biye ne da son Allah (SWT).
Imamun Nabahani ya ce, “Ziyarar kabarin Annabi (SAW) ita ce mafi girman kusanci zuwa ga Allah, ita ce mafi kaunar da’a ga Allah, ita ce hanyar da mutum zai bi ya samu kololuwar daraja. Duk wanda ya butulce ya ce ba haka ba, ya tube igiyar Musulunci daga wuyarsa. Kuma ya saba wa Allah, ya saba wa Annabi (SAW), ya saba wa tarin jama’ar malaman Musulunci na Allah.”
Alkadiy Iyad ya ce “Ziyarar Annabi (SAW) Sunnah ce daga sunnonin da Musulmi suka gaje ta kuma wacce aka hadu a kanta, falala ce abar kwadaitarwa.”
Darakudni ya ruwaito Hadisi daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ziyarci kabarina cetona ya wajaba a kansa.” Har ila yau, Darakudnin ya ruwaito daga Hadisin Abdullahi bin Umar (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ziyarce ni bayan rasuwata kamar ya ziyarce ni ne ina cikin rayuwata”.
Zainuddin ibnil Husainil Maragiyu ya ce “Ya wajaba ga Musulmi ya kudurta cewa ziyarar Manzon Allah (SAW) kusanci ce; ibada ce saboda wadancan Hadisan guda biyu. Da kuma fadin Allah a cikin Alkur’ani cewa “da al’ummarka za su zalunci kansu sai su zo ma su nemi gafarar Allah a wajenka, kai kuma ka nema masu gafara, za su samu Allah mai karbar tuba da jinkai ne”.
Malamin sai ya kara da cewa “Manzon Allah (SAW) ya nema mana gafara, abin da ya rage sai mu je wurinsa, idan muka je sai mu nemi gafarar a gabansa. Shikenan abubuwa guda uku sun cika – mun je wurinsa, mun nemi gafara, ya nema mana gafara.”
Don haka, Alhajin da ya je ziyara kafin Arfa ya riga ya samu gafara tun kafin ranar Arfa sai ya zama garabasa biyu. Wanda kuma ya je bayan Arfa, abin da ya rage na daga zunubinsa da ya yi kafin zuwa ziyarar sai ya nemi gafarar a gaban Manzon Allah (SAW).
Ana so mai ziyara ya lizimci ladabi da kankar da kai, ya sunkuyar da ganinsa a yayin da yake ziyarar Annabi (SAW). Ya ji a ransa cewa ya zo wurin Annabi (SAW) kuma ga shi nan kamar yana ganinsa. Saboda babu banbanci tsakanin ziyararsa yana da rai da kuma bayan wafatinsa. Sannan mai ziyara ya rika tuna irin yadda su Sayyidina Abubakar (RA) suke ladabi a gabansa da magana a hankali. Kar mai ziyara ya yi kuru-kuru da ido, babu ladabi, babu natsuwa a tare da shi. Kar mutum ya kuskura ya bi maganganu wadanda suke raina janibinsa (SAW). Lamarin Annabi (SAW) ba na wasa ba ne, a kula da kyau.
Kuma ya kamata gwamnati ta kula da kyau, a rika samun jagororin mahajjata masu tsoron Allah da soyayyar Manzon Allah (SAW) don fadakar da Alhazai kan abin da ya fi zama daidai a Musulunci da Imani. Amma ba sharrori da munanan fahimta wanda da zarar mutum ya ji, ya san kiyayyar Manzon Allah (SAW) ce kawai ake koyar da mahajjata ba.
Hatta ita kanta Saudiyya yanzu abin ya dame ta, nema take ta gyara.
Akwai wasu da suke neman hana zuwa Madina ma kwata-kwata. Ko kuma su takura wa Alhazai a kan kar su yi kwana takwas din nan duk da cewa akwai Hadisi ingantacce kan haka.
Hadisin ba wai ya zo da adadin kwana takwas ne ba, amma yawan sallolin da Hadisin ya fada na adadin kwana takwas ne kamar yadda za mu kawo yanzu.
An karbo daga Anas bin Malik (RA), Annabi (SAW) ya ce “Duk wanda ya yi sallah a Masallacina guda arba’in ba tare da wata sallah ta tsere ma sa ba, za a rubuta ma sa takardar shaidar cewa ya kubuta daga wuta da duk wata azaba. Kuma zai kubuta daga munafunci.” Ahamdu bin Hambali ya ruwaito, shi ma Dabarani ya ruwaito da ingantaccen sanadi.
Idan aka buga lissafin sallolin farilla guda biyar da muke da su a rana, jimillar sallah 40 za ta zama ta kwana takwas.
Ya kamata a rika barin Alhazai suna samun wannan falalar. Abu ne da ya inganta a cikin Sunnar Annabi (SAW).
Kai ma mai ziyara ka san cewa ba hutu da shantakewa kawai za ka yi a Madina ba, ka yi kokari ikamar kowace sallah kar ta kubuce ma a Masallacin Annabi (SAW) idan ba akwai lalura mai karfin gaske ba.
Za mu dakata a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa insha Allahu. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi hakka kadirihi wa mikdarihil aziym.