ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 29, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ziyarar Kabarin Annabi SAW (3)

by Sulaiman and Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
4 years ago
Kabarin Annabi SAW

LABARAI MASU NASABA

Falalar Yawaita Istigifari (2)

Falalar Salatut Tasbihi

Ci gaba daga makon jiya…

Imamul Fakihani, ya ce “wurin da aka binne Manzon Allah (SAW) ya fi sama ya fi kasa”. Haka nan, Alkadiy Iyad ya ce “Babu wani wurin da ya kai a hada shi da wurin da aka binne jikin Manzon Allah (SAW) saboda abu biyu: na farko, cewar da aka yi ko wane mutum ana binne shi a kasar da aka yi shi da ita, to nan wurin da aka binne Manzon Allah (SAW) kasar jikinsa ne, to wane abu ne za a iya hada shi da jikinsa (SAW)? Na biyu, bisa irin Mala’ikun da suke sauka a nan wurin, da irin albarkar da take sauka, da salatin da ake aikawa da sauran alheran da ke sauka a wurin, babu wani wurin da ya kai shi.”
Abu Ya’ala ya ruwaito Hadisi daga Sayyidina Abubakar (RA) ya ce, ya ji Manzon Allah (SAW) ya ce “Allah ba ya karbar Annabinsa sai a wurin da Annabin ya fi so.” Sayyidina Abubakar ya fadi Hadisin ne lokacin da Annabi (SAW) ya yi wafati sa’ilin da aka samu sabani kan wuri mafi dacewa a binne shi (SAW). Saboda haka suka ce babu shakka wurin da Annabi (SAW) ya fi so, nan ne Allah ya fi so. Domin son sa, yana biye ne da son Allah (SWT).
Imamun Nabahani ya ce, “Ziyarar kabarin Annabi (SAW) ita ce mafi girman kusanci zuwa ga Allah, ita ce mafi kaunar da’a ga Allah, ita ce hanyar da mutum zai bi ya samu kololuwar daraja. Duk wanda ya butulce ya ce ba haka ba, ya tube igiyar Musulunci daga wuyarsa. Kuma ya saba wa Allah, ya saba wa Annabi (SAW), ya saba wa tarin jama’ar malaman Musulunci na Allah.”
Alkadiy Iyad ya ce “Ziyarar Annabi (SAW) Sunnah ce daga sunnonin da Musulmi suka gaje ta kuma wacce aka hadu a kanta, falala ce abar kwadaitarwa.”
Darakudni ya ruwaito Hadisi daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ziyarci kabarina cetona ya wajaba a kansa.” Har ila yau, Darakudnin ya ruwaito daga Hadisin Abdullahi bin Umar (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ziyarce ni bayan rasuwata kamar ya ziyarce ni ne ina cikin rayuwata”.
Zainuddin ibnil Husainil Maragiyu ya ce “Ya wajaba ga Musulmi ya kudurta cewa ziyarar Manzon Allah (SAW) kusanci ce; ibada ce saboda wadancan Hadisan guda biyu. Da kuma fadin Allah a cikin Alkur’ani cewa “da al’ummarka za su zalunci kansu sai su zo ma su nemi gafarar Allah a wajenka, kai kuma ka nema masu gafara, za su samu Allah mai karbar tuba da jinkai ne”.
Malamin sai ya kara da cewa “Manzon Allah (SAW) ya nema mana gafara, abin da ya rage sai mu je wurinsa, idan muka je sai mu nemi gafarar a gabansa. Shikenan abubuwa guda uku sun cika – mun je wurinsa, mun nemi gafara, ya nema mana gafara.”
Don haka, Alhajin da ya je ziyara kafin Arfa ya riga ya samu gafara tun kafin ranar Arfa sai ya zama garabasa biyu. Wanda kuma ya je bayan Arfa, abin da ya rage na daga zunubinsa da ya yi kafin zuwa ziyarar sai ya nemi gafarar a gaban Manzon Allah (SAW).
Ana so mai ziyara ya lizimci ladabi da kankar da kai, ya sunkuyar da ganinsa a yayin da yake ziyarar Annabi (SAW). Ya ji a ransa cewa ya zo wurin Annabi (SAW) kuma ga shi nan kamar yana ganinsa. Saboda babu banbanci tsakanin ziyararsa yana da rai da kuma bayan wafatinsa. Sannan mai ziyara ya rika tuna irin yadda su Sayyidina Abubakar (RA) suke ladabi a gabansa da magana a hankali. Kar mai ziyara ya yi kuru-kuru da ido, babu ladabi, babu natsuwa a tare da shi. Kar mutum ya kuskura ya bi maganganu wadanda suke raina janibinsa (SAW). Lamarin Annabi (SAW) ba na wasa ba ne, a kula da kyau.
Kuma ya kamata gwamnati ta kula da kyau, a rika samun jagororin mahajjata masu tsoron Allah da soyayyar Manzon Allah (SAW) don fadakar da Alhazai kan abin da ya fi zama daidai a Musulunci da Imani. Amma ba sharrori da munanan fahimta wanda da zarar mutum ya ji, ya san kiyayyar Manzon Allah (SAW) ce kawai ake koyar da mahajjata ba.
Hatta ita kanta Saudiyya yanzu abin ya dame ta, nema take ta gyara.
Akwai wasu da suke neman hana zuwa Madina ma kwata-kwata. Ko kuma su takura wa Alhazai a kan kar su yi kwana takwas din nan duk da cewa akwai Hadisi ingantacce kan haka.
Hadisin ba wai ya zo da adadin kwana takwas ne ba, amma yawan sallolin da Hadisin ya fada na adadin kwana takwas ne kamar yadda za mu kawo yanzu.
An karbo daga Anas bin Malik (RA), Annabi (SAW) ya ce “Duk wanda ya yi sallah a Masallacina guda arba’in ba tare da wata sallah ta tsere ma sa ba, za a rubuta ma sa takardar shaidar cewa ya kubuta daga wuta da duk wata azaba. Kuma zai kubuta daga munafunci.” Ahamdu bin Hambali ya ruwaito, shi ma Dabarani ya ruwaito da ingantaccen sanadi.
Idan aka buga lissafin sallolin farilla guda biyar da muke da su a rana, jimillar sallah 40 za ta zama ta kwana takwas.
Ya kamata a rika barin Alhazai suna samun wannan falalar. Abu ne da ya inganta a cikin Sunnar Annabi (SAW).
Kai ma mai ziyara ka san cewa ba hutu da shantakewa kawai za ka yi a Madina ba, ka yi kokari ikamar kowace sallah kar ta kubuce ma a Masallacin Annabi (SAW) idan ba akwai lalura mai karfin gaske ba.
Za mu dakata a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa insha Allahu. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi hakka kadirihi wa mikdarihil aziym.

Kabarin Annabi SAW
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Martani Game Da Yiwuwar Kara Kudaden Da Amurka Ke Kashewa Da Nufin Dakile Tasirin Kasar Sin
  • Sulaiman
    Gwamna Sule Ya Halarci Ƙaddamar da Kamfanin Jinlide•Qiangyu New Energy, Ya Ƙara Jaddada Aniyar Jawo Masu Zuba Jari
  • Sulaiman
    Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Fitar Da Takarda Game Da Matsayin Sin Kan Abin Da Ake Kira “Samar Da Kayayyaki Fiye Da Kima”
  • Sulaiman
    Ba Ma Fatan Wani Ɗan Nijeriya Ya Kwana da Yunwa — Remi Tinubu
Kabarin Annabi SAW
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ posts Bio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Istigifari (2)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Salatut Tasbihi
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Falalar Yawaita Istigifari (2)
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Istigifari (2)

July 24, 2026
Falalar Salatut Tasbihi
Dausayin Musulunci

Falalar Salatut Tasbihi

July 17, 2026
Kabarin Annabi SAW
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 3, 2026
Next Post
Barka Da Sabuwar Shekarar Hijira: Adamu Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Mallaki Katin Zaɓe

Barka Da Sabuwar Shekarar Hijira: Adamu Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Mallaki Katin Zaɓe

LABARAI MASU NASABA

WAFCON 2026: Nijeriya Ta Sha Kashi A Hannun Malawi

WAFCON 2026: Nijeriya Ta Sha Kashi A Hannun Malawi

July 29, 2026
Cinikin Salah Zuwa Besiktas Ya Rushe

Cinikin Salah Zuwa Besiktas Ya Rushe

July 29, 2026
Mun Yi Ƙoƙarin Sasanta Iran Da Amurka A Lokacin Gasar Kofin Duniya – Infantino

Mun Yi Ƙoƙarin Sasanta Iran Da Amurka A Lokacin Gasar Kofin Duniya – Infantino

July 29, 2026
Sin Ta Yi Martani Game Da Yiwuwar Kara Kudaden Da Amurka Ke Kashewa Da Nufin Dakile Tasirin Kasar Sin

Sin Ta Yi Martani Game Da Yiwuwar Kara Kudaden Da Amurka Ke Kashewa Da Nufin Dakile Tasirin Kasar Sin

July 29, 2026
Gwamna Sule Ya Halarci Ƙaddamar da Kamfanin Jinlide•Qiangyu New Energy, Ya Ƙara Jaddada Aniyar Jawo Masu Zuba Jari

Gwamna Sule Ya Halarci Ƙaddamar da Kamfanin Jinlide•Qiangyu New Energy, Ya Ƙara Jaddada Aniyar Jawo Masu Zuba Jari

July 29, 2026
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Fitar Da Takarda Game Da Matsayin Sin Kan Abin Da Ake Kira “Samar Da Kayayyaki Fiye Da Kima”

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Fitar Da Takarda Game Da Matsayin Sin Kan Abin Da Ake Kira “Samar Da Kayayyaki Fiye Da Kima”

July 29, 2026
Sana’ar Ƙosai: Remi Tinubu Ta Yi Kira ga Burna Boy da Davido Su Taimaka wa Talakawa

Ba Ma Fatan Wani Ɗan Nijeriya Ya Kwana da Yunwa — Remi Tinubu

July 29, 2026
Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Dakatar Da INEC Game Da Soke Rajistar ADC Da Wasu Jam’iyyu

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Umarnin Cire Rajistar ADC Da Wasu Jam’iyyu Huɗu

July 28, 2026
Kayayyaki Masu Fasahar AI Sun Zamo Sabbin Abubuwa Masu Tasiri A Cinikin Waje Na Kasar Sin

Kayayyaki Masu Fasahar AI Sun Zamo Sabbin Abubuwa Masu Tasiri A Cinikin Waje Na Kasar Sin

July 28, 2026
Ruwa

2027: Gwamnan Kaduna Ya Sanar Da Sabon Mataimakinsa A Zaɓen Gwamna

July 28, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.