A ranar 1 da 2 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a sabbin wuraren al’adun kasar Sin biyu a jere, wato gidan adana tsoffin littattafai na kasar Sin, da kuma kwalejin nazarin tarihin kasar Sin.
Gidan adana tsoffin littattafai na kasar Sin, ya adana littattafai masu daraja da aka gada a da can, wadanda suka kunshi al’adun al’ummar Sinawa. Kwalejin nazarin tarihin kasar Sin kuwa, na nazari, da yin cikakken bayani game da asalin al’adun al’ummar Sinawa.
A yayin ziyarar, shugaba Xi Jinping ya bayyana aniyarsa game da ziyarar, inda ya ce, a zamanin da muke ciki, wato zamanin dake da wadatar kasa da zaman lafiyar al’umma, ana da karfin tabbatar da al’adun al’ummar kasa.
Shugaba Xi Jinping, ya dora muhimmanci sosai ga kiyaye al’adun gargajiya na al’ummar Sinawa, da gadon su, da kuma yin kirkire-kirkire da samun bunkasuwa a wannan fanni.
Ya jaddada cewa, don raya al’adun al’ummar Sinawa na zamani, ya kamata a kiyaye imanin tabbatar da al’adu, da kiyaye bin hanyar da ta dace, da kuma samun ‘yancin kai a fannin tunanin al’ummar kasa. (Zainab)